Connect with us

News

Wani Mutum Ya Shiga Hannun Ƴansanda Bisa Zargin Hallaka Maƙwabcinsa Da Adda Akan  Kuɗi

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Wani mutum mai suna Lekan Oyebamiji ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin kashe maƙwabcinsa, Samson Gabriel, da adda sakamakon saɓanin kan  kuɗi a garin Akinlalu da ke Jihar Osun.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar, lokacin da mutanen biyu suka samu saɓani kan kuɗi, wanda ya rikide zuwa faɗa.

Mun San Duk Irin Kokarin Da Suke Yi Domin Ganin INEC Ta Cire Dantakararmu Na Gwamna A  Kano —Kwankwaso 

Wani mazaunin yankin, Tayo Rasheed, ya shaida wa jaridar PUNCH cewa wanda ake zargin ya yi amfani da adda wajen farmakar Gabriel, inda ya yi masa munanan raunuka a sassa daban-daban na jikinsa har ya mutu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Osun, Abiodun Ojelabi, ya ce an kama wanda ake zargin, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.

Ya bayyana cewa mutanen biyu maƙwabta ne, kuma saɓanin kuɗi ne ya haddasa rikicin da ya kai ga mutuwar Gabriel.

Advertisement

A cewarsa, wanda ake zargin ya ɗauki addarsa ne a lokacin gardamar, inda ya farmaki marigayin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending