News
Mun San Duk Irin Kokarin Da Suke Yi Domin Ganin INEC Ta Cire Dantakararmu Na Gwamna A Kano —Kwankwaso
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi wasu ’yan hamayya da ƙoƙarin ganin an cire sunan ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, daga jerin sunayen ’yan takarar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa.
Kwankwaso, wanda ke takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu matasan Kwankwasiyya a gidansa da ke Miller Road, a Kano.
Zargin nasa na zuwa ne kwana guda bayan da INEC ta wallafa sunayen ’yan takarar gwamnan Kano a shafinta na intanet, ba tare da sanya sunan Gwarzo ba.
Sai dai wata majiya daga INEC ta shaida wa TRT Afrika Hausa a ranar Asabar cewa, rashin sanya sunan ɗan takarar ba daga hukumar ya samo asali ba, domin batun yana gaban kotu.
Majiyar ta ce da zarar kotu ta warware matsalar, hukumar za ta mayar da sunan ɗan takarar cikin jerin sunayen.
Da yake magana kan lamarin, Kwankwaso ya ce suna da yaƙinin samun nasara a kotu, yana mai cewa irin wannan yanayi ya taɓa faruwa a zaɓen shekarar 2019.
“Mun yi imanin za mu yi nasara a kotu, domin ba yau ne karon farko da irin wannan abu ya faru ba.
“A shekarar 2019 ma, sai ranar Litinin kotu ta wanke Abba (ɗan takararmu), alhali zaɓe zai gudana ranar Asabar, kuma muka yi nasara,” in ji shi.
Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwarsa kan nasarar shari’ar, duk da rashin sanya sunan Gwarzo a jerin sunayenda INEC ta fitar.

