News
NAF Ta Fitar Da Sunayen Mutane 25 Da Suka Mutu A Haɗarin Jirgin Soji
Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta fitar da sunayen mutane 25 da suka rasa rayukansu a haɗarin jirgin saman rundunar da ya afku a ranar Litinin a Igbokoda, Jihar Ondo.
Mutanen da suka mutu sun haɗa da ma’aikatan jirgin guda biyar da wasu fasinjoji 20.
2027: INEC Za Ta Bayyana Matsayarta Kan Takarar Pantami, Nami, Adamu A Yau
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar Sojin Saman Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya sanya wa hannu, rundunar ta ce jirgin na kan hanyarsa ta komawa Legas ne bayan kammala wani aiki a Benin lokacin da hatsarin ya afku.
NAF ta tabbatar da cewa babu wani mutum da ya tsira daga hatsarin, inda ta ce an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana zaman makoki domin alhinin mutanen da suka rasa rayukansu, yayin da aka buɗe littafin ta’aziyya a hedikwatar NAF da ke Abuja.
Rundunar ta ce manyan jami’an gwamnati, jami’an diflomasiyya, shugabannin hukumomin tsaro da sauran al’umma na iya rubuta saƙonnin ta’aziyyarsu ga iyalan mamatan da kuma rundunar.
Sunayen ma’aikatan jirgin
1. Squadron Leader MI Aburime – Matuƙin jirgin
2. Squadron Leader AP Man-Ugwueje – Mataimakin matuƙin jirgi
3. Flight Lieutenant IS Bako – Mataimakin matuƙin jirgi
4. Warrant Officer Abubakar A – Injiniyan jirgi
5. Corporal Uguru HC – Injiniyan jirgi
Sunayen fasinjojin
1. Flight Lieutenant TL Lazarus
2. Flight Lieutenant M Akinloye
3. Flying Officer IM Adeshina
4. Master Warrant Officer Onwuka F
5. Master Warrant Officer Matini BA
6. Warrant Officer Nuhu FS
7. Flight Sergeant James RB
8. Flight Sergeant Mohammed AI
9. Sergeant Ani AE
10. Sergeant Izibenikien SI
11. Sergeant Alafuka C
12. Sergeant Mbadugha AN
13. Lance Corporal Ugwuba FC
14. Lance Corporal Eledan GE
15. Mrs Ezeh Nneka
16. Godstmine Tarabina
17. Joy Micheal
18. Sunday Micheal
19. Ukeme David
20. Gideon Omotola
Rundunar Sojin Saman ta ce za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani da ya shafi binciken musabbabin hatsarin.
