Connect with us

News

Za Ka Iya Aikata Kusan Duk Wani Laifi Ka Tsallake Hukunci A Najeriya, Idan Kana Da Kyakkyawar Alaƙar Siyasa ” —  Sarki Sanusi ‎

Published

on

images (1)

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce mutum na iya tsallake hukunci kan kusan duk wani laifi a Najeriya idan yana da alaƙa ko goyon bayan manyan masu iko a siyasa.

‎Sarkin ya bayyana hakan ne a wata hira da Channels Television a Legas, yayin gabatar da wani littafi mai mujalladi uku mai suna “Unexplained Wealth: A Trilogy of Nigerian Financial Law”, wanda lauya mai yaƙi da rashawa, Dr Wahab Shittu, SAN, ya rubuta.

‎An Yi Garkuwa Da Fiye Da Mutum 80 A Cikin Mako Biyu A Arewacin Nijeriya — Rahoto 

‎Sarkin ya ce yin bitar dokokin da ake da su domin gano giɓinsu da kuma samar da hanyoyin magance matsalar dukiyar da ba a san tushenta ba na da matuƙar muhimmanci.

‎Sai dai ya ce gyaran dokoki kaɗai ba zai wadatar ba, matuƙar ba a inganta yadda ake aiwatar da su ba.

‎A cewarsa, Najeriya na da hukumomi da kotuna da aka ɗora wa alhakin bincike, gano tare da gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata laifukan rashawa.

Advertisement

‎Sai dai ya nuna damuwa kan yadda al’amuran siyasa da alaƙar wasu mutane da masu iko ke iya yin tasiri a yadda ake gudanar da bincike da shari’o’in da suka shafi rashawa.

‎Sanusi ya ce an samu wasu lokuta da ake tuhumar mutane da laifukan rashawa, amma daga baya a janye ko a yi watsi da tuhume-tuhumen saboda alaƙarsu da wani ɓangare na siyasa ko kuma samun goyon bayan wasu masu ƙarfi.

‎Ya kuma ambaci batun tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin wani misali da ya ce ya haifar da tambayoyi game da yadda ake amfani da tsarin shari’a wajen gudanar da irin waɗannan lamura.

‎Sarkin ya ce irin waɗannan abubuwa na iya sa jama’a su fara tambayar ko da gaske ana yaƙi da rashawa ne, ko kuma ana amfani da tsarin shari’a wajen cimma wasu manufofin siyasa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending