Labarai
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wata Mata Da Wasu Mutum Uku Kan Zargin Kashe Yaron Kishiyarta Saboda Gado A Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wata mata da wasu mutane uku bisa zargin haɗa baki wajen yin garkuwa da wani yaro mai shekaru 14 tare da kashe shi, domin ɗanta tilo shi kaɗai ya gaji dukiyar mahaifinsa.
Yaron mai suna Mahmoud Auwal, an yi garkuwa da shi ne a ranar 20 ga Afrilu, 2026, bayan wani matashi mai suna Muhammad Musa Isma’il, mai shekaru 20, mazaunin unguwar Sharada a Kano, ya yaudare shi.
Shugaban Kasar Mongolia Ya Yi Murabus Sakamakon Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Rundunar ’yan sandan ta ce ta fara binciken lamarin ne bayan wata mata mazauniyar unguwar Danbare da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ta kai rahoton ɓacewar ɗanta a ranar 29 ga Afrilu, 2026.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta bayyana cewa binciken da sashen yaƙi da garkuwa da mutane ya gudanar ya kai ga kama Isma’il a ranar 3 ga Nuwamba, 2026.
A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya yaudari yaron, sannan ya ambaci wasu mutane biyu, Abubakar Muhammad Isah, mai shekaru 27, da Auwal Muhammad, mai shekaru 26, a matsayin waɗanda suka haɗa baki da shi.
A cewar rundunar, waɗanda ake zargin sun haɗa baki wajen kashe yaron, kafin su bar gawarsa a wurin. Daga bisani, jami’an ’yan sanda na sashen Kwalli suka gano gawar tare da kai ta ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Kwararru na Sir Muhammad Sunusi.
Ƙarin bincike ya kai ga kama Hajiya Rukayya Auwal, mai shekaru 20, mazauniyar Mararaba da ke ƙaramar hukumar New Karu ta jihar Nasarawa, wadda rundunar ta bayyana a matsayin wadda ake zargin ta shirya aikata laifin.
’Yan sandan sun ce ana zargin Rukayya, wadda kishiya ce ga mahaifiyar yaron, da shirya kawar da ’ya’yan mijinta huɗu domin ɗanta tilo shi kaɗai ya gaji dukiyar mahaifinsu.
Haka kuma, rundunar ta yi zargin cewa matar ta ɗauki wasu ’yan daba domin su kai wa Isma’il hari a jihar Nasarawa, a wani yunƙuri na hana shi tona asirin lamarin.
Rundunar ta ce za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi Allah-wadai da kisan tare da tabbatar wa iyalan mamacin cewa rundunar za ta tabbatar da an yi adalci.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
