Connect with us

Labarai

JIGAWA: Matashi Ya Rasa Ransa Yayin Kare Iyayensa Daga Harin ’Yan Bindiga

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani matashi mai shekaru 30, Lawan Yahaya, bayan ya yi ƙoƙarin kare iyayensa daga harin da suka kai musu a gidansu da ke Ƙaramar Hukumar Garki ta Jihar Jigawa.

Maharan, waɗanda yawansu ya kai kusan bakwai, sun kuma raunata mahaifinsa da mahaifiyarsa a yayin harin.

DSS Ta Roƙi Kotu Ta Ci Tarar SERAP Naira Miliyan 100

Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Tsaro ta Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) a Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya fitar, ta tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar sanarwar, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:50 na safiyar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026, a unguwar Nabai Fulani da ke mazabar Kargo.

Sanarwar ta ce maharan, ɗauke da bindigogin AK-47, sun kutsa cikin gidan wani dattijo mai suna Yahaya Jibrin, mai shekaru 70, inda suka far masa da matarsa, Zainab Yahaya, mai shekaru 45.

Advertisement

Bayan kammala harin, maharan sun tsere da wani babur ƙirar Boxer marar lambar rajista, tare da wasu kuɗaɗe waɗanda ba a bayyana adadinsu ba.

An garzaya da iyayen zuwa Babban Asibitin Garki domin ba su kulawar likitoci, yayin da aka tabbatar da mutuwar Lawan Yahaya.

Daga bisani, an miƙa gawarsa ga iyalansa domin gudanar da jana’izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci.

Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, CC Muhammad Kabiru Ingawa, ya yi Allah-wadai da harin tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ƙara ƙaimi wajen haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa tsaro da kuma kamo waɗanda suka aikata laifin.

Haka kuma, ya yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko mutum da suke zargi ga jami’an tsaro mafi kusa, domin taimakawa wajen dakile ayyukan miyagu a jihar.

Advertisement

 

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending