Labarai
Gobara Ta Yi Ajalin Wasu Sabbin Ma’aurata A Filato

Wasu sabbin ma’aurata, Sikiru Habib da matarsa, Ramlat Lawan, sun rasu sakamakon gobarar da ta tashi a gidansu da ke Anguwan Miyango, Bukuru, ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na daren Asabar, lokacin da ma’auratan ke barci a cikin ɗakinsu.
Wani maƙwabcinsu, Injiniya Lawal Suleiman, ya shaida wa Daily Trust cewa an garzaya da ma’auratan asibiti bayan ceto su daga cikin ɗakin da gobarar ta kama.
Ya ce an samu matsala ne lokacin da ƙofar ɗakin ta ƙi buɗewa, lamarin da ya sa ma’auratan suka makale yayin da wutar ke ci gaba da yaɗuwa.
Suleiman ya ce matasa mazauna unguwar sun yi ƙoƙarin ceto su, inda daga bisani suka samu damar shiga ɗakin ta taga tare da fitar da su kafin jami’an kashe gobara su iso.
An kai ma’auratan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) domin ba su kulawar gaggawa.
Sai dai ya ce an fara samun labarin rasuwar ango a ranar Lahadi, yayin da amaryar ta rasu a ranar Litinin.
Mazauna yankin sun yi zargin cewa tashin wutar na iya kasancewa sakamakon ƙarfin lantarkin da ya wuce kima, duk da cewa hukumomi ba su tabbatar da musabbabin gobarar ba.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
