Labarai
DSS Ta Roƙi Kotu Ta Ci Tarar SERAP Naira Miliyan 100

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja da ta tabbatar da hukuncin tarar Naira miliyan 100 da aka yanke wa ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta SERAP bisa zargin ɓata sunan jami’anta biyu.
DSS ta gabatar da buƙatar ne a gaban kotun yayin da SERAP ke ƙalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) ta yanke mata.
A nata ɓangaren, SERAP ta roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙarar da ta soke hukuncin, tana mai neman a yi watsi da tarar da aka kakaba mata.
Kotun ta tanadi hukunci bayan sauraron ƙorafe-ƙorafen ɓangarorin biyu, inda za ta sanar da ranar yanke hukuncin nan gaba.
Tun da farko, Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja ta samu SERAP da laifin ɓata sunan jami’an DSS biyu da suka kai ziyara ofishin ƙungiyar a ranar 9 ga Satumba, 2024.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa jami’an sun mamaye ofishinta a lokacin ziyarar, lamarin da ya haifar da takaddama tsakanin ɓangarorin biyu.
Kotun ta kuma umarci SERAP da ta biya tarar Naira miliyan 100 tare da wallafa takardar neman afuwa ga DSS a bainar jama’a bisa hukuncin da ta yanke.
Sai dai SERAP ta ƙalubalanci hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara, yayin da DSS ke neman kotun ta tabbatar da hukuncin da aka yanke tun farko.
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
