Connect with us

News

KANO: An Kama Wani Matashi Kan Zargin Buga Takardun Indigene Na Bogi A Karamar Hukumar Dala 

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Ƙaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Habibu Abdullahi, mai shekaru 30, bisa zargin ƙirƙira da buga takardun shaidar zama ɗan asalin ƙaramar hukumar (Indigene) na bogi a yankin Kurna.

Jami’in Ofishin Indigene na ƙaramar hukumar, Yahaya Musa Jibrin, ya bayyana cewa an gano lamarin ne bayan gabatar da wata takardar shaidar zama ɗan asali da ta gaza tantancewa.

Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna

Ya ce binciken da aka gudanar ya kai ga gano wanda ake zargin, wanda aka kama a ranar 13 ga Oktoba, 2026, kafin daga bisani a miƙa shi ga ’yan sanda domin gudanar da bincike da ɗaukar matakan shari’a.

Bayan gurfanar da shi a gaban kotu, an bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali yayin da ake ci gaba da shari’ar.

A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙaramar Hukumar Dala, Malam Suraj Ibrahim Imam, ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani aiki da ya saɓa wa doka ko ya yi barazana ga sahihancin takardun gwamnati ba.

Advertisement

Ya jaddada muhimmancin kiyaye sahihancin takardun hukuma tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifin karya doka zai fuskanci matakan da suka dace.

Lura: Ana zargin wanda aka kama ne, kuma shari’ar na ci gaba. Saboda haka, ba a ɗauke shi a matsayin wanda aka tabbatar da laifinsa ba har sai kotu ta yanke hukunci.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending