News
Gwamnatin Kano Ta Haramta Wa Masu “Chemists” Yin Karin Ruwa Da Karin Jini
Gwamnatin Jihar Kano ta haramta wa shagunan sayar da magunguna, da aka fi sani da Chemists, yin karin ruwa ta jijiya (IV) da kuma ƙarin jini a faɗin jihar.
Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu ta jihar (PHIMA) ce ta bayyana hakan, tana mai cewa Chemists ba su da izinin gudanar da ayyukan da suka yi kama da na asibiti, ciki har da yin karin ruwa da ƙarin jini.
Gwamnatin Kano Ta Musanta Zargi Ware N235.4m Domin Gina Makarantar Da Ba Ta Wanzu Ba A Sumaila
Jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Fauziyya Habib Mahmoud, ce ta fitar da sanarwar, inda ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin kare lafiyar al’umma.
Mukaddashiyar Sakatariyar Zartarwa ta PHIMA, Hajiya Khadijah Hussein Sa’id, ta ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa ayyukan kula da lafiya ana gudanar da su ne a wuraren da suka dace, ƙarƙashin kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
Ta ce duk wani Chemist ko asibiti da aka kama yana gudanar da karin ruwa ko ƙarin jini ba bisa ƙa’ida ba, za a rufe shi nan take, sannan a ɗauki matakin da doka ta tanada.
Hukumar ta kuma gargadi masu Chemists da su dakatar da ayyukan, tana mai cewa ba za ta yi wa masu karya ƙa’idojin afuwa ba.
PHIMA ta roƙi jama’a da su kai rahoton duk wani wuri da ake gudanar da irin waɗannan ayyuka ba bisa ƙa’ida ba zuwa ofishinta da ke Magaji Rumfa. Ta ce masu kai rahoton za su iya gabatar da shaidu kamar hotuna ko rasit.
An bayyana matakin ne a wani taro da hukumar ta shirya wa masu asibitoci masu zaman kansu kan yadda ake rubutawa da adana bayanan marasa lafiya.
A cewar PHIMA, karin ruwa da ƙarin jini ayyuka ne da aka takaita ga asibitocin da hukumomin da suka dace suka amince da su, kuma dole ne ƙwararrun ma’aikatan lafiya su kasance suna kula da marasa lafiyar.
