Sports
Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila Karon Farko Tun Bayan Shekara 22
Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila Karon Farko Tun Bayan Shekara 22
Wannan na zuwa ne bayan da Manchester City ta yi 1-1 da Bournemouth a wasa mako na 37 da suka buga a ranar Talata.
Kenan wasa daya ya rage a kammala kakar wasannin shekarar 2025/2026.
Mace Mafi Kankanta A Duniya Da Ta Lashe Kundin Bajinta Na Guiness Na Mai Tallan Kaya Kawa
Duk da haka Arsenal ta bai wa Manchester City ta zarar makin da ko City ta yi nasara a wasan karshe, ita kuma Arsenal an doke ta to sun zama zakarun bana.
Kakar wasanni ta shekarar 2003/2004 ita ce ta karshe da Asenal ta lasar gasar Firimiyar Ingila, wato shekara 22 kenan.
A lokacin ta yi nasara a wasa, 26 da kunnan doki 12, tare da bayar da tazarar maki 11 a lokacin.
Yanzu haka dai saura wasa daya a kammala kakar bana, inda Arsenal za ta karbi kofin da ta lashe a bikin da za a gudanar a filin West Ham United.
Ita kuwa Manchester City za kece raini da Aston Villa a mako mai zuwa a kakar wasannin ta shekarar 2025/2026.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
