News
Haɗurran Ababen Hawa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 1,347 Cikin Watanni Uku —Rahoto
Akalla mutane 1,347 ne suka mutu sakamakon haɗurran ababen hawa da suka afku a sassan Najeriya cikin watanni uku na farkon shekarar 2026.
Alƙaluman Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya sun nuna cewa mace-macen sun faru ne sakamakon haɗurran ababen hawa da aka samu a faɗin ƙasar tsakanin watan Janairu da Maris na wannan shekara.
Abin Mamaki: An Gano Mahaifa a Jikin Wani Namiji Mai Shekara 26
Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke fama da yawaitar haɗurran ababen hawa, inda rashin bin dokokin hanya, gudun wuce gona da iri, tukin ganganci da kuma rashin kyawun wasu hanyoyi ke daga cikin abubuwan da ake dangantawa da faruwar haɗurran.
Haka kuma, masana kan harkokin sufuri sun sha bayyana cewa rashin kyawun hanyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen haddasa haɗurran ababen hawa a sassan ƙasar.
A shekarar 2025 ma, alkaluma sun nuna cewa mutane 5,289 sun rasa rayukansu sakamakon haɗurran ababen hawa 10,446 da suka faru a faɗin Najeriya.
A makon da ya gabata kuma, wani mummunan hatsarin mota a jihar Filato ya yi sanadin mutuwar mutane 20.
Rahotanni sun ce ababen hawa huɗu, da suka haɗa da motoci biyu, babur guda da kuma motar dakon kaya, ne suka yi karo da juna a hatsarin.
Yawaitar haɗurran ababen hawa na ci gaba da janyo asarar rayuka da dukiyoyi a Najeriya, lamarin da ke ƙara jaddada buƙatar bin dokokin hanya da kuma inganta hanyoyin sufuri a faɗin ƙasar.
