Connect with us

News

Abin Mamaki: An Gano Mahaifa a Jikin Wani Namiji Mai Shekara 26

Published

on

ckqutjk8 surgery 625x300 12 September 26

Likitoci a birnin Delhi na ƙasar Indiya sun gano cewa wani magidanci mai shekaru 26 yana ɗauke da mahaifa da bututunta a cikin jikinsa, bayan ya shafe kusan shekaru biyu da aure ba tare da samun ɗa ba.

Magidancin ya garzaya asibiti domin neman gano dalilin da ya sa shi da matarsa ba su samu haihuwa ba tun bayan aurensu.

Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano Ta Gayyaci Tijjani Gandu kan Zargin Karya Doka

A yayin da likitoci ke gudanar da bincike da gwaje-gwaje kan lafiyarsa, sai aka gano cewa yana da mahaifa da kuma bututun da ke haɗe da ita a cikin ƙashinsa na ƙugu.

Sai dai likitocin sun bayyana cewa a zahiri, yanayin jikinsa na waje na namiji ne, kuma yana da dukkanin siffofin jikin namiji. Haka kuma, babu wata alama ta zahiri da za ta nuna cewa yana ɗauke da mahaifa.

Dr Sushil Kharbanda, shugaban sashen kula da mafitsara a wani asibiti mai zaman kansa da ke Delhi, shi ne ya jagoranci kula da majinyacin.

Advertisement

A cewarsa, binciken da aka gudanar domin gano musabbabin rashin haihuwarsa ne ya kai ga gano mahaifar da bututunta a cikin jikinsa.

Ya ce lamarin ya kasance abin mamaki ga likitocin, kasancewar majinyacin yana da kamannin namiji a zahiri, yayin da binciken cikin jikinsa ya nuna kasancewar wasu gabobin haihuwa na mace.

 

 

NDTV

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending