Sports
Arsenal ta lallasa Liverpool a gasar firimiya ta Ingila
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Arsenal ta lallasa Liverpool da ci 3-1 a karawar da suka yi a gasar firmiya ta Ingila, nasarar da ta taimakawa kungiyar rage tazarar dake tsakanin kungiyoyin biyu.Kafin karawar dai Liverpool ke matsayi na farko da maki 51, yayin da Arsenal ke matsayi na 3 da maki 46.
Wannan nasarar ta sa Arsenal ta samu karin maki 3, abinda ya kawo adadin makin ta zuwa 49 da kuma karbe matsayi na 2 daga hannun Manchester City wadda ke da kwantan wasanni guda 2.
Direba ya murkushe yaro yayin da yake kokarin arce wa jami’an kwastam
Bukayo Saka ya fara jefawa Arsenal kwallon ta na farko a minti 14 da fara wasa, yayin da Gabriel ya farkewa Liverpool a minti 48 lokacin da yaci gida cikin kuskure.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Gabriel Martinelli ya jefawa Arsenal kwallon ta na 2 a minti na 67, yayin da Trossard ya ci wa Arsenal kwallon ta na 3 a minti 92.
‘Dan wasan tsakiya na Arsenal, Jorginho yace kwallo guda da Liverpool ta samu a wasan bai karya musu gwuiwa ba, sai dai kara musu kaimi wajen ganin sun yi abinda ya dace domin samun nasara.
Shi kuwa Declan Rice cewa yayi sun san muhimmancin wasan a gare su, shi yasa suka jajirce wajen ganin sun samu nasara a kan Liverpool wadda ta yi musu illa a watan Disamba.
Kafin karawar Arsenal da Liverpool, Manchester United ta doke West Ham United da ci 3-0, nasarar da ta kai ta matsayi na 6 da maki 38, sai kuma Wolverhampton Wanderers da ta doke Chelsea da ci 4-2, nasarar da ta mayar da ita matsayi na 10 a tebur da maki 32, yayin da Chelsea ke matsayi na 11 da maki 31.
