Sports
Liverpool ta lallasa Manchester United Da Ci 3-0 A Gaban Magabata
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Liverpool ta lallasa Manchester United da ci 3-0 a karawar da suka yi a yammacin yau a gaban magabata.
Diaz ya jefawa Liverpool kwallaye guda 2 a mintina 35 da 42, ya yin da Mohammed Salah ya kafa ‘dan ba a kan nasarar sakamakon kwallo ta 3 da ya jefa a minti 56.
Sama Da Mutane 10,000 Ne Suka Rasa Matsugunansu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Zamfara.
Wannan gagarumar nasara ta bai wa Liverpool damar komawa matsayi na 2 a teburin Firimiya da maki 9 kamar Manchester City wadda ita ma take da maki 9, sai dai ta fi Liverpool zirara yawan kwallaye.
Wannan koma bayan shi ne na 2 da United ta samu a sabuwar kakar lura da cewa a makon jiya ta barar da wasan ta da Brighton Albion.
A yanzu haka ta na matsayi na 14 a tebur da maki 3 kacal. Sauran wasannin da aka yi yau na Firimiya sun nuna cewar an tashi 1-1 tsakanin Chelsea da Crystal Palace, ya yin da Newcastle ta samu nasara a kan Tottenham Hotspur da ci 2-1.
Reuters