Sports
Jamus Ta Taimakawa ‘Yar Wasan Najeriya Da Aron Keke Domin Shiga Gasar Olympics
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kasar Jamus ta taimakawa wata ‘yar tseren kekunan Najeriya da keken hawa domin shiga gasar Olympics dake gudana a birnin Paris yanzu haka.
‘Yar Najeriyar Ese Lovina Ukpeseraye tace an sanya sunanta cikin gasar ne a kurarren lokaci, kuma bata da keken da zata hau lokacin gasar, abinda ya sa ta bayyana ba tare da keken ba.
TABARMAR KUNYA: Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki Ya Yi Amai Ya Lashe
Wannan ya sa tawagar ‘yan wasan Jamus suka taimaka mata da keken. A sakon da ta aike ta kafar X, Ukpeseraye ta jinjinawa Jamus saboda yadda suka taimaka mata.
Ukpeseraye ce ‘yar Najeriya ta farko da ta wakilci kasar a tseren kekuna na wasannin Olympics.
Advertisements
