Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Hallaka Kanal Din Soja A Gidansa Da Ke Abuja

Published

on

Wani jami’in soja mai muƙamin Kanal, Abdussalam Ude, ya rasa ransa bayan wasu yan bindiga sun kai hari gidansa da ke unguwar Kurudu a Abuja.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, jim kaɗan bayan ya dawo daga wurin aiki.

‎Gwamnati Ta Na Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro ‎ ‎—Tsohon sufetan ƴan sandan Najeriya Mike Okiro

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa maharan sun yi ƙoƙarin sace Kanal ɗin ko kuma wani daga cikin iyalansa.

A yayin harin ne suka harbe shi har lahira, yayin da matarsa, direbansa da jami’in tsaronsa suka samu raunukan harbin bindiga, kuma aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

Kanal Ude, wanda ya fito daga Jihar Enugu, ya kasance jami’i a Nigerian Army Intelligence Corps, inda ya riƙe muƙamai masu muhimmanci a fannin tattara bayanan sirri da yaƙi da ta’addanci.

Advertisement

Ya kuma taɓa aiki a ayyukan soji a Arewa maso Gabashin Najeriya da kuma ƙasashen Chadi da Faransa.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labari, Rundunar Sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da jami’an tsaro suka fara bincike domin gano waɗanda suka kai harin da kuma dalilansu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending