Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna

Published

on

WhatsApp Image 2026 08 27 at 17.04.24

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta cafke wani mutum da ake zargi da safarar makamai, tare da kwato bindigogi da harsasai 637 a wasu samame da ta gudanar a sassan jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kaduna. Ya ce nasarorin da rundunar ta samu sun samo asali ne daga bayanan sirri da kuma kokarin jami’anta wajen dakile ayyukan ta’addanci da sauran laifuka.

Rasuwar Ugboaja Babban Rashi Ne Ga Ƙungiyar NLC— Abbas Ibrahim

Kwamishinan ya ce a ranar 25 ga watan Agusta, jami’an rundunar da ke sashen Sabon Gari sun cafke wani mutum mai shekaru 39, mai suna Kenneth, dan asalin Jihar Delta, a tashar motoci ta Yan’Karfe da ke Zariya, bayan samun bayanan sirri kan ayyukansa.

Ya ce binciken buhun da wanda ake zargin yake dauke da shi ya kai ga gano bindigogi kirar AK-49 guda biyu, harsasan RPG guda 228, harsasan AK-47 masu girman 7.62mm guda 275, cajar AK-47 guda biyar da wasu abubuwa da ake zargin miyagun kwayoyi ne.

CP Muhammad ya kuma ce a ranar 24 ga watan Agusta, jami’an rundunar sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da kasancewa ’yan bindiga a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Advertisement

Ya bayyana wadanda aka cafke da sunayen Ibrahim Muhammad, wanda aka fi sani da “Alti”; Usman Tukur, wanda ake kira “Mallam”; da Hassan Alhaji Salisu, wanda aka fi sani da “Tagwaye”. A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa mambobin wata kungiyar ’yan bindiga ne da ke gudanar da ayyukanta a Millennium City da sauran sassan Jihar Kaduna.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar ta kwato harsasan AK-47 guda 134 daga hannun wani mai babur da aka tsayar a hanyar Kachia a ranar 25 ga watan Agusta. Ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa wani fitaccen dan bindiga da ake kira “Yellow Mai-Million” ne ya aike shi domin karbar harsasan da kai masa.

A wani samame kuma, rundunar ta cafke Gideon Martins na Sabon Tasha, inda aka same shi da bindiga kirar gargajiya mai harsasai biyu, mari, harsashin 9mm guda daya, harsasan bindiga guda biyu, na’urar POS, na’urar hako rami da kuma kayan jami’an tsaro.

Rundunar ta kuma cafke wasu mutane uku bisa zargin aikata fashi da makami da cin zarafin mata a yankunan Rafin Tukurwa da Zariya. Haka kuma, jami’an tsaro sun gano buhuna 11 dauke da busassun ganyaye da ake zargin tabar wiwi ce a kan hanyar Zariya zuwa Kano.

A wani samame na daban, jami’an ’yan sanda na Kajuru sun cafke Barnabas Amale, mai shekaru 27, bisa zargin satar waya da kuma yin barazanar harbi da bindiga. Rundunar ta kuma kwato wata motar Toyota Hilux mallakin Hukumar Ruwa ta Kaduna da aka sace daga Ungwan Rimi, Kaduna, bayan bin diddigin motar har zuwa Kano.

Haka kuma, CP Muhammad ya ce rundunar ta cafke Abdullahi Abubakar da Shehu Sani bisa zargin kai hari da lalata kayayyakin Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa da ke Mando, Kaduna. Ya ce ana zargin mutanen da daure jami’an tsaro biyar tare da lalata na’urar samar da wutar lantarki ta cibiyar.

Advertisement

Kwamishinan ya ce rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri da sauran dabarun tsaro wajen cafke masu aikata laifuka tare da gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending