News
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
Tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Alhaji Suleiman Abba, ya ce ya shiga siyasa ne domin ya ci gaba da yi wa al’umma hidima tare da mayar musu da wani ɓangare na abin da ya samu a tsawon rayuwarsa ta aikin gwamnati.
Suleiman Abba, wanda ke neman kujerar Sanatan Yankin Dutse a Jihar Jigawa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a yayin bikin cika shekaru 80 da kafuwar Radio Kano ranar Asabar.
Tsohon IGP Abba Ya Nemi Kafa Cibiyar Horar Da ’Yan Jarida A Radio Kano
Ya ce ya gode wa Allah da ya ba shi damar yin aiki a rundunar ’yan sanda, inda ya samu damar hawa matakai har zuwa matsayin Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya.
Tsohon IGP ɗin ya ce hidimarsa ga al’umma ba ta fara ne da shiga rundunar ’yan sanda ba, domin ya taɓa aiki a Radio Kano a matsayin ma’aikacin wucin-gadi.
Ya ce lokacin da ya nemi aikin Radio Kano, an ɗauke shi ne bisa cancanta, ba tare da amfani da wata alaka ko tasirin wani mutum ba.
Alhaji Abba ya kuma tuna wasu daga cikin muhimman mukaman da ya riƙe a rundunar ’yan sanda, ciki har da Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Rivers da kuma kwamandan MOPOL a Abuja.
Ya ce bayan ya kammala aikinsa a rundunar ’yan sanda, ya fahimci cewa har yanzu yana da wata gudummawa da zai iya bayarwa ga al’umma ta hanyar shiga hidimar jama’a.
“Na shiga siyasa ne domin in mayar wa al’umma wani ɓangare na abin da na samu daga gare su,” in ji shi.
Tsohon IGP ɗin ya kuma waiwayi zaɓen shekarar 2015, inda ya ce lokacin ya kasance mai matuƙar ƙalubale ta fuskar siyasa da tsaro, lamarin da ya buƙaci ingantaccen jagoranci da haɗin kan jami’an tsaro.
