Connect with us

News

Mun Sha Fitsarinmu Don Mu Tsira Da Ranmu — Wanda Ya Tsira Daga Mutuwar Mutane 37 A Neja

Published

on

Wanda aka tattauna da shi

Wani mutum da ya tsira daga mutuwar mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ne a hannun jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) a Jihar Neja, Dauda Shehu, ya bayyana irin halin ƙunci da suka shiga kafin mutuwar mutanen.

Dauda ya bayyana hakan ne a wata hira da kafar Zarar Bunu TV, inda ya ce an kulle mutane 66 a cikin ɗaki guda, lamarin da ya jefa su cikin matsanancin zafi da ƙarancin iska.

Kunkurun Fadar Alaafin Na Oyo Mai Shekaru 420 Ya Mutu

Ya ce yayin da zafin ɗakin ya ƙaru, wasu daga cikin mutanen da har yanzu suke da ƙarfi suka riƙa buga ƙofar ɗakin suna neman agaji, amma ba a saurare su ba.

“Mun yi duk abin da za mu iya domin mu rayu, har muka sha fitsarinmu saboda ba mu da ruwa. Wasu daga cikin mutanen da ke kusa da mu suka fara faɗuwa ɗaya bayan ɗaya,” in ji Dauda.

Ya ce lamarin ya samo asali ne bayan wasu shugabannin al’umma a Lokoto, da ke Ƙaramar Hukumar Bosso, suka buƙaci a biya naira 150,000 kan kowane ramin haƙar ma’adinai, kuɗin da wasu daga cikin matasan suka kasa biya.

Advertisement

Wani da ya tsira, Aminu Sale — ba sunansa na ainihi ba — ya ce ɗan gudun hijira ne daga Allawa a Ƙaramar Hukumar Shiroro, kuma haƙar ma’adinai ce hanyar da yake samun abin da zai dogara da shi.

A halin yanzu, iyayen wasu daga cikin waɗanda suka mutu suna roƙon hukumomi da su miƙa musu gawawwakin ’ya’yansu domin a yi musu jana’iza.

Malam Abdullahi, wani uba, ya ce ya shafe kwanaki uku yana ƙoƙarin ganin an saki ɗansa, amma hakan bai yiwu ba. Ya ce ya kai wa ɗansa abinci da daddare, sannan ya sake komawa da safe, sai ya tarar da ɗansa ya mutu.

“Na rasa wanda yake ciyar da iyalina,” in ji shi.

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending