News
Kashi 61 Cikin 100 Na ‘Yan Nijeriya Da Suka Mallaki Hankalinsu Na Cikin Matsanancin Rashin Kudi —Rahoto
Wani sabon rahoto ya bayyana cewa kashi 61 cikin 100 na yan Nijeriya da suka mallaki hankalinsu na cikin matsanancin rashin Kudi, duk da ƙaruwa da aka samu wajen amfani da sabbin hanyoyin gudanar da harkokin kuɗi na zamani.
Rahoton Access to Financial Services in Nigeria (A2F) 2026, wanda ƙungiyar Enhancing Financial Inclusion and Advancement (EFInA) ta gudanar, ya mayar da hankali kan yadda ’yan Nijeriya ke samun damar ayyukan kuɗi, yadda suke amfani da su da kuma yadda suke tinkarar matsalolin tattalin arziki.
NEJA: Mutane 33 Sun Mutu A Hannun jami’an NSCDC
Binciken ya nuna cewa matsin kuɗi na ci gaba da shafar wani kaso mai yawa na manyan ’yan ƙasar, duk da cewa samun damar amfani da wasu ayyukan kuɗi na zamani da na dijital na ƙara yaɗuwa.
Rahoton ya kuma nuna cewa kashi 71.6 cikin 100 na mutanen da suka fuskanci matsalar kuɗi sun dogara da wasu hanyoyin magance matsalar da ka iya ƙara jefa su cikin mawuyacin hali na kuɗi.
Daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen shawo kan matsin kuɗin akwai karɓar bashi, amfani da kuɗin da aka tanada da kuma sayar da kadarori domin biyan buƙatun yau da kullum.
A gefe guda, EFInA ta ce amfani da ayyukan kuɗi na dijital na ƙara yaɗuwa, lamarin da ke nuna yadda fasahar kuɗi ke samun karɓuwa a tsakanin ’yan Nijeriya.
Ƙungiyar ta ce sakamakon binciken zai taimaka wajen fahimtar yadda ’yan Nijeriya ke samun damar ayyukan kuɗi da kuma irin hanyoyin da suke amfani da su wajen tinkarar matsalolin tattalin arziki.
