Uncategorized
Mutum Na Uku Ya Mutu Bayan Jirgin Sama Ya Dauko Sauro Daga Afirka Zuwa Jamus
Wani mutum ya mutu a Jamus sakamakon zazzabin cizon sauro, inda adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon cutar da ake dangantawa da filin jirgin saman Frankfurt ya kai uku.
Hukumomin lafiya sun ce mutumin na zaune ne a yankin Schwanheim, da ke kusa da filin jirgin saman Frankfurt.
Yadda Kwararowar Kasuwannni Da Kasuwanci Cikin Unguwa Ke Barazana Ga Unguwar Fagge
Mutuwar tasa ta biyo bayan rasuwar wasu ma’aikatan filin jirgin biyu da suka mutu sakamakon cutar a watan Yuli da Agusta.
A wannan makon, hukumomi sun kuma tabbatar da wasu mutane biyu da suka kamu da zazzabin cizon sauro a Schwanheim.
Rahotanni sun ce mutanen ba su yi balaguro zuwa wuraren da cutar ta fi yaɗuwa ba, kuma ba sa aiki a filin jirgin saman Frankfurt, lamarin da ya sa hukumomi ke zargin cewa sauro mai ɗauke da cutar ne ya shigo Jamus ta jirgin sama.
Hukumomi na zargin sauro nau’in Anopheles ne, wanda ke iya ɗauke da ƙwayar cutar malaria. Cibiyar Robert Koch ta Jamus ta ce irin wannan sauro na iya yin tafiyar kilomita biyar zuwa 10.
A irin wannan yanayi, sauro mai ɗauke da ƙwayar cutar na iya shiga jirgin sama daga wata ƙasa, sannan ya fita a filin jirgin ko yankunan da ke kusa da shi, inda zai iya cizon mutane.
Hukumomin lafiya sun ce irin wannan yanayi ba kasafai yake faruwa a Jamus ba. Sai dai an kafa tarkunan kama sauro a filin jirgin saman Frankfurt domin gano nau’in sauro da kuma binciken inda ya fito.
