News
Jami’an EFCC Sun Gano Matatar Man Fetur Da Wasu ‘Yan China Ke Gudanarwa A Ogun
Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta Najeriya (EFCC) ta gano wata matatar man fetur da ake zargin wasu ’yan ƙasar China ne ke gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba a yankin Ogere da ke Jihar Ogun.
Hukumar ta ce jami’anta sun kai samame matatar ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, bayan samun bayanan sirri da kuma sa ido kan ayyukan tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba.
Jami’an Ƴansanda 98 Ne Suka Mutu A cikin Watanni 10 A Sassan Najeriya — Rahoto
A cewar EFCC, jami’an sun tarar da wurin babu kowa a lokacin da suka isa, lamarin da ya nuna cewa babu wanda ke gudanar da ayyukan a lokacin.
Sai dai sun gano ragowar kayayyakin da ake amfani da su wajen tace man fetur, da kuma wasu tankunan da aka binne a ƙarƙashin ƙasa.
Hukumar ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin gano waɗanda ke da hannu a gudanar da matatar domin ɗaukar matakan da suka dace.

