Uncategorized
Bauchi: Ɗalibin Sakandare Ya Baje Kolin Motar Gas, Jirgin Sama Da Sauran Ƙirƙire-Ƙirkirensa
Daga Sani Saleh Chinade da Sani Gazas Chinade, Damaturu
Wani ɗalibin aji uku na ƙaramar sakandare a Ummul-Qura Science Academy da ke Azare, Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi, Hayatuddeen Sadik Bello, ya ƙera wasu na’urori da nufin taimakawa wajen sauƙaƙa rayuwar al’umma.
Ɗalibin ya baje kolin wasu daga cikin abubuwan da ya ƙera ne a lokacin bikin bayar da kyaututtuka ga ɗaliban da suka yi fice a karatu da haddar Alƙur’ani da makarantar ta shirya a harabarta da ke Azare.
Yadda Kwararowar Kasuwannni Da Kasuwanci Cikin Unguwa Ke Barazana Ga Unguwar Fagge
Daga cikin abubuwan da Hayatuddeen ya ƙera akwai murhun girki mai amfani da ruwa da fetur, samfurin jirgin Jet, jirgi mai saukar ungulu, mota mai amfani da iskar gas, jirgin ruwa da injin niƙa.
Da yake bayyana burinsa, Hayatuddeen ya ce yana son ƙirƙirar wasu fasahohi da za su taimaka wajen rage wahalhalun rayuwar yau da kullum da al’umma ke fuskanta.
Ya ce yana da burin ƙirƙirar wata fasaha da za ta samar da makamashi ta amfani da kashin shanu, da kuma motar kashe gobara, musamman domin rage dogaro da man fetur da iskar gas.
“Burina nan gaba shi ne samar da sabbin hanyoyin kimiyya da za su sauƙaƙa wa al’umma ayyukan yau da kullum, tare da taimakawa wajen magance wasu matsalolin da suke fuskanta,” in ji shi.
Mahaifin ɗalibin, Abubakar Sadik Bello, ya bayyana farin cikinsa kan yadda ɗansa ya nuna hazaka a fannin kirkire-kirkire, yana mai cewa nasarar ba ta ɗansa kaɗai ba ce, har da iyalansa da makarantar.
“Wallahi ban san lokacin da hawaye suka zubo daga idona ba saboda tsananin farin cikin da na ji. A ganina wannan nasara ba ta ɗana kaɗai ba ce, nasara ce ta kowa,” in ji shi.
Ya gode wa Allah bisa baiwar da Ya ba ɗansa, tare da yabawa malaman Ummul-Qura Science Academy kan yadda suke taimaka wa ɗalibai wajen gano da bunƙasa baiwarsu.
Hukumar makarantar ta ce tana shirya irin wannan biki ne domin karrama ɗaliban da suka yi fice tare da ƙara musu ƙwarin gwiwa, da kuma zaburar da sauran ɗalibai su ƙara mayar da hankali kan karatunsu.
