Connect with us

News

Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano 

Published

on

20260904 134856 COLLAGE

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar Labour Party (LP), Alhaji Hamisu Santuraki, ya yi alkawarin kafa Hukumar Kula da Hayar Gidaje, idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027.

Santuraki ya ce manufar hukumar ita ce dakile ƙarin kuɗin haya ba bisa ƙa’ida ba da kuma kare ’yan haya daga cin zarafi da sauran matsalolin da suka shafi haya.

An Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Tsoratar Da Dagaci A Kano 

Ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakinsa, Comrade Abbas Ibrahim, inda ya ce hukumar ba za ta sanya farashin haya iri ɗaya ga dukkan gidaje ba, sai dai ta tsara farashi bisa la’akari da wurin da gida yake, irin gidan, girmansa, yanayinsa da kayan more rayuwa.

Ya ce za a yi rajistar masu gidaje da kadarorin haya, sannan a ba dillalan gidaje lasisi tare da tsara kuɗin dillanci da sauran ka’idojin gudanar da sana’ar.

Santuraki ya ƙara da cewa hukumar za ta samar da tsarin kai ƙorafi da sasanta rikicin haya, musamman kan ƙarin haya ba bisa ƙa’ida ba, korar ’yan haya, tsadar kuɗin dillanci da cin zarafi.

Advertisement

A cewarsa, za kuma a samar da wani Rent Transparency Portal, wanda zai bai wa jama’a damar tantance gidaje, masu gidaje da dillalan da aka ba lasisi, da kuma sanin farashin hayar da aka amince da shi.

Ya ce za a rika bitar farashin haya lokaci zuwa lokaci bisa la’akari da hauhawar farashi, kuɗin gini, darajar gidaje da yanayin kasuwar haya.

“Manufar ba ita ce azabtar da masu gidaje ba, sai dai samar da kasuwar haya mai cika da  adalci, inda ’yan haya za su biya kuɗi , yayin da masu gidaje su samu riba mai kyau,” in ji shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending