Uncategorized
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
DAGA MUHAMMAD KABIR, KANO
Daraktan Kudi na Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are (HJRBDA), kuma tsohon Kwamishina sau uku da tsohon Shugaban Karamar Hukuma sau biyu, Dr Musa Illiyasu Kwankwaso, ya ce rawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ayyukan raya ƙasa sun isa su sa ’yan Najeriya su ba shi damar yin wa’adi na biyu.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar kuma ya rabawa manema labarai ranar Laraba, inda ya ce yadda Shugaba Tinubu ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaɓen 2027, da kuma yadda ya gudanar da harkokin zaɓe ba tare da tsoma baki ba, na nuna cewa shugaban ɗan dimokuraɗiyya ne.
Malami Ɗaya Na Koyar Da Ɗaliban Firamare 54 A Najeriya —Rahoto
Ya ce ya kamata ’yan Najeriya su ba Tinubu damar kammala abin da ya fara na sake gina tattalin arziki da samar da abubuwan more rayuwa a faɗin ƙasar.
A cewarsa, a cikin shekaru ukun da gwamnatin Tinubu ta yi, shugaban ya nuna cewa ɗan kishin ƙasa ne da ke kula da ci gaban dukkan yankunan Najeriya.
Kwankwaso ya ce musamman a yankin Arewa, an samu ci gaba wajen yaƙi da rashin tsaro da kuma aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.
“Jiya ma, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa (AFAN), Dr Farouk, ya bayyana nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu wajen kwato wasu filayen noma daga hannun ’yan bindiga,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ɗaruruwan mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon rashin tsaro sun fara komawa gidajensu saboda ingantuwar tsaro a wasu yankuna.
A fannin ababen more rayuwa, Kwankwaso ya ce sama da kilomita 1,400 na manyan ayyukan tituna, tare da wasu manyan ayyukan makamashi da sufuri, na gudana a yankin Arewa, waɗanda darajarsu ta haura naira tiriliyan 7.21.
Ya lissafa sake gina babbar hanyar Abuja–Kaduna–Zariya–Kano, gyaran hanyar Kano–Maiduguri, faɗaɗa hanyar Kano–Katsina da kuma sake gina hanyar Kano–Hadejia cikin ayyukan gwamnatin tarayya da yake ganin sun cancanci a yaba.
Ya kuma ambaci shirin gina babbar hanyar Sokoto–Badagry mai tsawon kilomita 1,068, wadda aka tsara za a haɗa da layin dogo, yana mai cewa aikin zai taimaka wajen ƙarfafa alaƙar kasuwanci tsakanin Arewa da Kudancin ƙasar.
A fannin sufuri, ya ce aikin layin dogo na Kano–Kaduna da aka kiyasta darajarsa da dala biliyan 1.2, da layin Kano–Maradi, da kuma shirin layin dogo na Kaduna, za su taimaka wajen sauƙaƙa jigilar mutane da kayayyaki.
Ya kuma ambaci aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 1,350 a Gwagwalada, da ayyukan samar da makamashin hasken rana a Kaduna.
A cewarsa, waɗannan ayyuka na da muhimmiyar rawa wajen ƙara samar da wutar lantarki da bunƙasa masana’antu a yankin.
Kwankwaso ya ce ɗaga matsayin Babban Asibitin Misau zuwa Federal Medical Centre, inganta Reference Hospital da ke Kaduna da kuma farfaɗo da Kumpada Irrigation Project na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka wajen inganta kiwon lafiya da noma.
“Waɗannan ayyuka sun nuna cewa yankin na samun kulawa mai muhimmanci,” in ji shi.
Ya buƙaci ’yan Najeriya su bambanta tsakanin suka mai ma’ana da kuma abin da ya kira yaɗa labaran siyasa domin ɓata suna, yana mai kira ga ’yan Arewa da su mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027 domin ya ci gaba da ayyukan da ya fara.
-
News4 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News5 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News7 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
