Connect with us

News

Idan Da Gwamnatin Tarayya Na Son Murde Zaben Osun, Babu Abin Da Zai Hana Ta Murdewa — ‎ ‎Tsohon gwamnan Ekiti

Published

on

ayo fayose (1)

Tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose, ya bayyana zaben gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta a matsayin mai matukar sarkakiya, sannan gwamnatin Tarayya na da karfin murde zaben idan ta ga dama.

Fayose ya bayyana zaɓen a matsayin mai matuƙar zafi da fafatawa, yana mai cewa da wuya a iya hasashen wanda zai yi nasara kafin bayyana sakamakon.

Idan Da Gwamnatin Tarayya Na Son Murde Zaben Osun, Babu Abin Da Zai Hana Ta Murdewa — ‎ ‎Tsohon gwamnan Ekiti

Ya bayyana hakan ne a wata hira da TVC News, yayin da yake sharhi kan nasarar da Gwamna Ademola Adeleke ya samu, wadda ta ba shi damar yin wa’adi na biyu.

Tsohon gwamnan ya ce ya shafe lokaci a Osun kafin da kuma lokacin zaɓen, inda ya ziyarci kasuwanni da al’ummomi domin jin ra’ayoyin jama’a kai tsaye.

A cewarsa, abin da ya lura da shi ya nuna cewa zaɓen ya kasance kusa da juna, kuma kowane ɗan takara na da damar yin nasara.

Advertisement

Fayose ya ce rabon kuri’u a wasu yankuna, musamman Ede, ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Adeleke, inda ya bayyana cewa daga cikin tazarar kusan kuri’u 66,000 da Adeleke ya samu, kusan 46,000 sun fito ne daga Ede.

 

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending