Connect with us

News

Biyan Haƙƙoƙin Tsofaffin Kansiloli Ba Siyasa Ba Ne – Waiya

Published

on

1787146079173

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na biyan basussukan haƙƙoƙin tsofaffin kansilolin jihar ba wai don siyasa ba ne, illa ƙoƙari ne na tabbatar da adalci da biyan haƙƙin waɗanda suka yi wa al’umma hidima.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da shugabancin Ƙungiyar Tsofaffin Kansilolin Jam’iyyar APC (Maslaha) na Kano ta Arewa da Kano ta Kudu, da aka gudanar a Mumbayya House da ke Kano.

Idan Da Gwamnatin Tarayya Na Son Murde Zaben Osun, Babu Abin Da Zai Hana Ta Murdewa — ‎ ‎Tsohon gwamnan Ekiti

Ya ce tsofaffin kansilolin na daga cikin muhimman jakadun Gwamna Abba Kabir Yusuf na asali a matakin ƙasa, saboda irin gudunmawar da suka bayar tun kafin kafa tsarin siyasar da ake ciki a yanzu.

A cewar Waiya, gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da jin daɗin tsofaffin kansilolin tare da sanya su cikin harkokin da suka shafe su, yana mai cewa ƙwarewarsu da kusancinsu da al’umma na da matuƙar muhimmanci.

“Biyan haƙƙoƙinsu ba wai siyasa ce kawai ta sa aka yi hakan ba, manufa ce da ta samo asali daga zuciya da kishin ganin an biya mutane haƙƙinsu,” in ji shi.

Advertisement

Ya ƙara da cewa mutum idan ya yi alheri kuma ya yi haƙuri, lokaci zai zo da wannan alherin zai dawo gare shi, yana mai kira ga tsofaffin kansilolin da su kwantar da hankalinsu tare da ƙara haɗin kai.

Waiya ya tabbatar musu cewa babu wani babban mataki da Gwamna Yusuf zai ɗauka da ya shafe su ba tare da tuntubarsu ko sanya su cikin lamarin ba.

Ya kuma buƙaci tsofaffin kansilolin da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da kuma tallafa wa manufofin gwamnatin jihar domin ganin an samu nasarar shirye-shiryenta.

Kwamishinan ya ce bai shiga gwamnati ne domin tara dukiya ba, sai dai domin bayar da gudunmawar kuɗi, ƙarfi da ƙwarewarsa wajen taimaka wa Gwamna Yusuf wajen sauke nauyin da ke kansa na inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.

Ya ƙara da cewa duk wanda ya ga an fara wani aikin alheri a ƙarƙashin gwamnatin jihar, ya kamata ya bayar da gudunmawarsa wajen ganin an kammala shi, domin al’umma su amfana.

Ya jaddada cewa haɗin kan tsofaffin kansiloli da sauran masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen ƙarfafa manufofin gwamnati da kuma tabbatar da ci gaban Jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending