Connect with us

News

Watan Maulidi Lokaci Ne Na Yawaita Ibada Da Ayyukan Alheri – Dr Yunusa

Published

on

IMG 20260814 235740 295 768x644 (1)

DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM, KANO

An yi kira ga Musulmi da su yi amfani da watan Rabi’ul Awwal wajen yawaita addu’o’i, ibada da ayyukan alheri domin neman kusanci da Allah.

Kiran ya fito ne daga bakin Sarkin Shanun Sarkin Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Dr Abubakar Yunusa Mai Takama da Ma’aiki, yayin wata tattaunawa da wakiliyar MU, Zainab Kamal Ibrahim.

Biyan Haƙƙoƙin Tsofaffin Kansiloli Ba Siyasa Ba Ne – Waiya

Dr Yunusa ya bayyana Rabi’ul Awwal a matsayin wata mai muhimmanci ga al’ummar Musulmi, kasancewar watan da aka haifi Annabi Muhammad (S.A.W), yana mai cewa ya kamata Musulmi su yi amfani da lokacin wajen tunawa da rayuwarsa da koyarwarsa.

Ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da gudanar da ayyukan alheri a lokacin Maulidi, ciki har da sadaqa, ciyar da jama’a da taimakon mabukata, tare da kyautata mu’amala da juna.

Advertisement

Ya ce wannan ne karo na 12 da suke gudanar da bukukuwan Maulidi na tsawon kwanaki 30 a cikin watan Rabi’ul Awwal, inda ake gudanar da shirye-shiryen tunawa da koyarwar Annabi (S.A.W).

A nasa jawabin, Malam Muhammad Mahi Naniya, ya ce addu’a tana da matukar muhimmanci a rayuwar Musulmi, musamman a lokacin da mutum yake fuskantar kalubale ko wata bukata.

Ya ce ya kamata Musulmi ya mayar da addu’a wani bangare na rayuwarsa, tare da karanta addu’o’in da Annabi (S.A.W) ya koyar, musamman kafin mutum ya fita daga gidansa ko ya fara wani aiki.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su yi koyi da halaye da koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W), yana mai cewa hakan zai taimaka wajen gina al’umma mai kyawawan dabi’u da zaman lafiya.

A karshe, ya yi addu’ar Allah Ya ba Musulmi ikon bautarsa yadda ya kamata, Ya kuma sanya su cikin wadanda za su samu tsira da rahamarsa a duniya da lahira.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending