News
Kotun Daukaka Kara Ta Soke Hukuncin Da Ya Umarci INEC Ta Soke Rajistar Jam’iyyar ADC
Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta soke rajistar jam’iyyar ADC da wasu jam’iyyun siyasa huɗu.
Hukuncin ya fito ne bayan kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abba Mohammed, ya yanke cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar tun farko, saboda haka hukuncin da ta yanke ba shi da inganci.
Shugaba Tinubu Ya Ki Yadda Ya Gana Da Tawagar Shugaban Afirka Ta Kudu
Kotun ta kuma bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ta yi kuskure da ta ci gaba da yanke hukunci duk da umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara na dakatar da ci gaba da shari’ar, wanda ya haɗa har da dakatar da fitar da hukunci. Haka kuma, kotun ta ce wanda ya shigar da ƙarar bai da hurumin yin hakan a shari’ar.
Baya ga ADC, sauran jam’iyyun da hukuncin da aka soke ya shafa sun haɗa da Accord Party, AA, APP da ZLP, lamarin da ke nufin hukuncin da ya umarci INEC ta soke rajistarsu ya zama ba shi da wani tasiri.
