News
Malami Ɗaya Na Koyar Da Ɗaliban Firamare 54 A Najeriya —Rahoto
Wani sabon rahoto ya nuna cewa tsarin makarantun gwamnati na Najeriya na fuskantar matsananciyar ƙarancin malamai, inda malamai 592,077 ke koyar da ɗalibai kimanin miliyan 32 a faɗin ƙasar.
Bayanan, waɗanda aka samo daga Digital Nigeria Education Management Information System (DNEMIS) na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, sun nuna cewa jimillar ɗaliban da aka ƙidaya sun kai 31,827,244, lamarin da ke nufin cewa a matsakaici malami guda na kula da kusan ɗalibai 54.
Yadda Wutar Lantarki Ta Hallaka Mai Gyaran Transformer
Rahoton ya kuma nuna cewa matsalar ta fi tsanani a wasu jihohin Arewa, musamman Kano da Katsina.
A Kano, inda aka samu ɗalibai 5,226,239 a bayanan, malami guda na kula da ɗalibai kusan 88, yayin da a Katsina ɗalibai 1,920,270 ke karkashin malamai da ke da matsakaicin nauyin ɗalibai 87.4 ga kowane malami.
Baya ga ƙarancin malamai, bayanan sun nuna cewa akwai kuma matsin lamba kan ababen more rayuwa na makarantu. A ƙasa baki ɗaya, ɗalibai kusan 32 ne ke amfani da aji guda 60, lamarin da ke ƙara nuna girman matsalar da tsarin ilimin gwamnati ke fuskanta.
Kano ce ke da mafi yawan ɗaliban da aka samu a cikin bayanan, inda rahoton ya nuna cewa sama da miliyan 5.2 ne ke cikin makarantun gwamnati. Hakan ya sa matsalar ƙarancin malamai a jihar ta zama abin da ke buƙatar kulawa ta musamman.
Masana ilimi sun dade suna bayyana cewa yawan ɗalibai a aji ba tare da isassun malamai ba na iya yin illa ga ingancin koyarwa, fahimtar ɗalibai da kuma sakamakon karatunsu.
Domin rage matsalar, ana buƙatar gwamnatocin tarayya da jihohi su ƙara ɗaukar ƙwararrun malamai, musamman a yankunan da ke da yawan ɗalibai, tare da tabbatar da daidaitaccen rabon malamai tsakanin makarantu.
Haka kuma, ya kamata a ƙarfafa horas da malamai da samar musu da ingantattun kayan aiki da yanayin aiki, domin ƙara ƙarfafa sha’awarsu ta ci gaba da aikin koyarwa.
-
News4 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News5 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News7 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
