News
Almajirai 4 Sun Rasa Ransu Bayan Cin Kifi A Kano
Almajirai huɗu sun mutu a Jihar Kano bayan sun ci wani kifi da ake zargin ya gurɓata, yayin da wani ɗalibi ke kwance a asibiti yana karɓar magani.
Lamarin ya faru ne a Tsangayar Malam Iliyasu Mai Tsangaya da ke Kadage Sharifai, a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano.
Bai Kamata Ace Gwamnoni Su Rika Tare Wa A Jihohin Da Ba Nasu Ba Lokacin Zabe —Goodluck Jonathan
Matan sun haɗa da Abdulfatah Mohammed mai shekaru 15, Yusuf Nuhu mai shekaru 16, Buhari Iliyasu mai shekaru 14 da Ibrahim Muhammad mai shekaru 22.
Wani ɗalibi mai suna Auwalu Surajo, mai shekaru 18, ya tsira daga lamarin kuma yana samun kulawa a asibiti.
A cewar Shugaban Ƙungiyar Tsangaya Media Network, Gwani Sani Musa Nuhu, an garzaya da ɗaliban zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) bayan sun kamu da rashin lafiya.
Ya ce ɗaliban huɗun sun mutu a asibitin a daren Lahadi, 16 ga Agusta.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da abin da ya haddasa mutuwar ɗaliban ba, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin. Wasu rahotanni sun yi zargin cewa kifin na iya kasancewa yana ɗauke da gubar maganin bera, amma ba a tabbatar da hakan a hukumance ba.
Wani abokin marigayin, Malam Surajo Unguwar Gareji, ya ce yana wurin lokacin da ɗaya daga cikin ɗaliban ya fito da kifin da misalin ƙarfe 7:00 na safe.
Ya ce sun fara cin kifin tare, amma ya daina bayan ya ɗanɗana shi saboda ya lura cewa ɗanɗanonsa ba daidai yake ba.
Shi ma wani abokinsu mai suna Malam Umar ya ce ya ƙi cin kifin saboda ya yi zargin cewa ba shi da lafiya.
A cewarsa, jim kaɗan bayan ɗaliban sun ci kifin, huɗunsu suka suma tare da fama da matsananciyar rashin lafiya.
Daga nan ne aka sanar da malaminsu, wanda ya shirya kai su asibiti.
’Yan sanda sun fara bincike
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta fara bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar ɗaliban.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce marigayin ’yan asalin Ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar ne ta Jihar Jigawa, kuma sun je Kano ne domin karatun Alƙur’ani da haddace shi.
Ya ce rundunar za ta sanar da jama’a sakamakon binciken da zarar an kammala.
An binne gawarwakin marigayin bisa tsarin addinin Musulunci bayan samun izini daga hukumomin da abin ya shafa.
