Connect with us

News

Wutar Lantarki Ta Hallaka Wani Ma’aikaci Yayin Gyaran Transformer 

Published

on

image9 e1787079295347

Wani ma’aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki na MainPower Electricity Distribution Limited (MEDL), Samson Okechi, ya rasu bayan wutar lantarki ta kama shi yayin da yake aikin gyaran transformer a Jihar Enugu.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, a Eke, Ƙaramar Hukumar Udi ta jihar, da misalin ƙarfe 1 na rana.

Bai Kamata Ace Gwamnoni Su Rika Tare Wa A Jihohin Da Ba Nasu Ba Lokacin Zabe —Goodluck Jonathan

Mai magana da yawun kamfanin, Emeka Ezeh, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce marigayin shi ne jagoran tawagar Abor da ke ƙarƙashin gundumar Ninth Mile ta kamfanin.

A cewar Ezeh, Okechi yana aikin gyaran transformer mai ƙarfin 50kVA/11kV da aka ɗora a kan turke lokacin da wutar lantarkin ta same shi.

Ya ce an garzaya da ma’aikacin zuwa Asibitin Our Saviour da ke Ngwo domin ba shi agajin gaggawa, amma likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.

Advertisement

Sai dai kamfanin ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kashe Okechi ko kuma lamarin ya faru ne sakamakon zagon ƙasa.

 

 

PREMIUM TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending