Connect with us

News

Almajirai Shida Sun Rasu Sakamakon Kamuwa Da Cutar Sankarau.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Almajirai shida a makarantar Islamiyya ta Tsangaya da ke garin Udobo a karamar hukumar Gamawa a jihar Bauchi sun rasu  sakamakon kamuwa da cutar sankarau.

Advertisement

A cewar shugaban  riko na karamar hukumar Gamawa, Nairu Baukura, yace wasu  almajirai biyu daga makarantun Tsangaya suna karbar magani a asibitin Udobo yanzu haka.

Kamfanoni Ne Ya Kamata Su Biya Harajin Tsaron Intanet Ba Mutane Ba

Yayin da Baukura ya kasa tabbatar da adadin mutanen da abin ya shafa, ya bayyana cewa wasu dama sunyi  jinya kuma an  sallame su.

Advertisement

Channels ta ruwaito cewa barkewar cutar ta bazu a cibiyoyin Tsangaya guda uku da ke cikin karamar hukumar.

Dangane da lamarin, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi, Rilwanu Mohammed, ya tabbatar da cewa jihar na kokarin shawo kan cutar.

Advertisement

Ya bayyana cewa kananan hukumomi bakwai sun samu rahoton bullar cutar sankarau.

Mohammed ya bayyana cewa majinyatan da suka yi mu’amala da wadanda abin ya shafa ana ba su magunguna don hana yaduwar cutar.

Advertisement

Sai dai ya ce jihar ta samu damar yi wa mutane allurar rigakafi a kananan hukumomi biyu kawo yanzu.

Jami’in kiwon lafiyar ya yi gargadin cewa ana kamuwa da cutar ta hanyar tarurrukan jama’a, yana mai jaddada muhimmancin matakan kariya don dakile barkewar cutar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending