Connect with us

Entertainment

An Kaddamar Da Fim Din Gidan Iyalin Indomie Domin Fadakar Da Jama’a

Published

on

IMG 20260224 WA0004
Spread the love

Kamfanin shirya fina-finai na Blue Sound ya kaddamar da sabon fim dinsa mai suna Gidan Iyalin Indomie, a wani shiri da aka bayyana cewa an yi shi ne domin wayar da kan jama’a kan bambancin taliyar Indomie da sauran taliyar yara na wasu kamfanoni.

IMG 20260224 132732 230

Da yake bayani ga manema labarai, shugaban kamfanin, TY Shaban, ya ce fim din na dauke da sakon fadakarwa domin mutane su fahimci cewa Indomie suna ne na kamfani mai zaman kansa, kuma kayansa sun bambanta da na wasu kamfanoni.

Shugaba Tinubu Ya Tsige Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun

Advertisement

A cewarsa, mutane da dama na kiran kowace taliyar yara da sunan Indomie, alhali kuwa akwai bambanci ta fuskar inganci da kuma asalinta.

Ya kuma ce kamfanin su ya hada gwiwa da Indomie wajen samar da fim din domin karfafa wayar da kan jama’a kan yadda za su bambance kayayyakin asali da na wasu kamfanoni.

IMG 20260224 132718 816

A nata bangaren, jarumar fim din kuma mai shirya shirin, Radeeya Jibril, ta bayyana cewa an hada kwararrun jarumai domin isar da sakon fadakarwa ga al’umma.

Advertisement

Ta ce sau da dama ana samun mutane na neman Indomie a shaguna, amma a ba su wani nau’in taliyar daban, su karba suna ganin Indomie suka saya. A cewarta, manufar fim din ita ce taimakawa jama’a su gane bambancin.

Har ila yau, ta yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa taliyar yara na rage basira, tana mai cewa kamfanin Indomie ya shafe sama da shekaru 35 yana aiki a Najeriya ba tare da irin wannan zargi ba.

Masu shirya fim din sun kuma bayyana fatan cewa al’umma za su kalli shirin domin fahimtar sakon fadakarwa da yake dauke da shi.

Advertisement

A wajen kaddamar da fim din, kamfanin Blue Sound tare da hadin gwiwar Indomie sun shirya liyafar shan ruwa ga mahalarta taron, ciki har da jarumai, masu shirya fina-finai da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *