Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Tsige Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun

Published

on

IMG 20260224 WA0198

Shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tsige Sufeto Janar na ‘Yan Sandan ƙasar, Kayode Egbetokun, daga mukaminsa, kamar yadda majiyoyi daga cikin manyan jami’an tsaro da kuma Police Service Commission suka tabbatar.

Rahotanni sun ce an umurci Egbetokun da ya shirya takardun miƙa mulki bayan wata ganawa da ya yi da shugaban ƙasa a fadar shugaban ƙasa, inda ake sa ran ya kammala mika ragamar aiki nan ba da jimawa ba.

Advertisement

Falalar Da Ke Tattare Da Azumin Watan Ramadan

A cewar majiyoyi, an naɗa Tunji Disu a matsayin sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda. Kafin wannan naɗi, Disu shi ne Mataimakin Sufeto Janar mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda da ke Alagbon a Jihar Legas.

Advertisement

Wasu rahotanni sun ce an shawarci tsohon shugaban rundunar da ya sauka domin mayar da hankali kan lafiyarsa. Haka kuma, an ce wasu jami’an ‘yan sanda sun nuna goyon baya ga sauyin shugabancin.

Har zuwa yanzu, ba a fitar da cikakken bayani a hukumance kan dalilan sauyin ba, amma ana sa ran sabon shugaban rundunar zai fara aiki cikin gaggawa.

Advertisement

 

 

Advertisement

NIGERIAN TRACKER 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending