Connect with us

Opinion

MURNAR CANDY: ‘Yaga Unifom Da Lalata Kayan Makaranta Ba Murna Ba Ce’ — Mu’azam Gezawa

Published

on

IMG 20260709 WA0007

Wani shugaban makarantar sakandare a Jihar Kano, Mu’azam Aminu Gezawa, ya yi gargaɗi ga ɗaliban da ke shirin kammala karatun sakandare da su guji gudanar da bikin da aka fi sani da “Candy”, yana mai cewa al’adar na haddasa lalacewar tarbiyya kuma tana jawo fushin Allah.

Mu’azam, wanda kuma shi ne Mai Binciken Kuɗi (Auditor) na Ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) ta Makarantar First Lady Secondary School, ya bayyana hakan ne a wani taron wayar da kan ɗaliban da za su kammala karatunsu, wanda aka gudanar a ranar Alhamis a harabar makarantar.

Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji 

A cewarsa, manufar taron ita ce ilmantar da ɗalibai kan illolin da ke tattare da bikin Candy, tare da ƙarfafa musu gwiwar su kammala karatunsu cikin mutunci da bin doka.

Ya ce daga cikin abubuwan da ake yawan aikatawa yayin bikin akwai yaga kayan makaranta, rubuce-rubuce a jikin unifom, kaɗe-kaɗe, hawa saman gine-gine, hayaniya da kuma lalata kayayyakin makaranta.

“Waɗannan ɗabi’u ba su dace da tarbiyyar ɗalibai ba, kuma suna jefa rayuka da dukiyoyi cikin haɗari,” in ji shi.

Advertisement

Shi ma da yake jawabi, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Iyaye da Malamai, Ni’imatullahi Bashir Saeed, ya ce an shirya taron ne domin faɗakar da ɗaliban da za su kammala karatu kan muhimmancin kauce wa duk wani abu da zai iya bata sunan makaranta ko iyayensu.

Ya kuma yi kira ga iyaye su ci gaba da sanya ido kan ‘ya’yansu tare da ba su tarbiyya mai nagarta domin su zama shugabanni na gari a nan gaba.

A nata ɓangaren, Shugabar Makarantar First Lady Secondary School, Hajiya Atine Muhammad, ta yabawa Ƙungiyar Iyaye da Malamai bisa shirya taron, tana mai bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tarbiyya a makarantar.

Ta ce wannan ne karo na farko da aka shirya irin wannan taron tun bayan kafuwar makarantar, inda ta bayyana fatan cewa zai taimaka wajen rage ayyukan rashin ɗa’a da wasu ɗalibai ke aikatawa bayan kammala jarabawar ƙarshe.

Hajiya Atine ta kuma gode wa Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano bisa goyon bayan da take bai wa makarantar, tare da kira ga sauran ƙungiyoyin iyaye da malamai su yi koyi da irin wannan shiri domin inganta tarbiyya da ɗabi’u a tsakanin ɗalibai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending