News
Cutar Kwalara Ta Hallaka Akalla Mutum 74 A Borno
Cutar kwalara da ta fara ɓarkewa a farkon watan Mayun 2026 a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 74 sannan wasu mutum 7,800 sun sake kamuwa, lamarin da ya yi wa cibiyoyin lafiya katutu, a cewar ƙungiyar agajin likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF).
MSF ta ce zuwa ranar 7 ga Yuni, an samu jimillar mutane 7,850 da ake zargin sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi 14 na jihar, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Borno ta bayyana. Ƙungiyar ta ce adadin masu kamuwa da cutar na ƙaruwa cikin sauri a kowace rana.
Ɓarkewar cutar na ƙara wa tsarin kiwon lafiya da tuni yake cikin mawuyacin hali nauyi, a yankin da ke fama da matsalolin tsaro sakamakon hare-haren masu tayar da ƙayar baya da kuma yawan mutanen da suka rasa matsugunansu, abin da ke ƙara haɗarin yaɗuwar cutar zuwa wasu wurare.
MSF, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Borno, ta buɗe cibiyar kula da masu fama da kwalara a Maiduguri domin tallafa wa ƙoƙarin da ake yi na shawo kan annobar.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News4 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
