News
Cutar Kwalara Ta Hallaka Mutane 108, Sama Da 13,000 Sun Kamu A Borno
Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a Jihar Borno ya kai 108, yayin da fiye da mutum 13,000 suka kamu da cutar tun bayan fara bazuwarta a watan Mayun 2026.
Rahoton da Ma’aikatar Lafiya da Kula da Lafiyar Jama’a ta Jihar Borno ta fitar ya nuna cewa zuwa ranar 18 ga watan Yuni, an tabbatar da kamuwar mutum 13,234 da cutar a sassa daban-daban na jihar.
Gwamnatin Oyo Ta Sanya Dokar Hana Fita A Kananan Hukumomi 10 Saboda Matsalar Tsaro
Bayanan sun nuna cewa daga cikin mutum 108 da suka mutu, 71 sun rasu ne a cibiyoyin kiwon lafiya yayin da wasu 37 suka mutu a cikin al’umma kafin su samu kulawar likitoci.
Rahoton ya ƙara da cewa annobar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 17 daga cikin 27 da ke faɗin jihar, lamarin da ke nuna yadda cutar ke ci gaba da yaɗuwa a yankuna da dama.
Birnin Maiduguri ne ya fi yawan waɗanda suka kamu da cutar, inda aka samu mutum 7,083, sai Ƙaramar Hukumar Jere da mutum 3,403. Haka kuma, ƙananan hukumomin Konduga da Monguno na daga cikin wuraren da annobar ta fi ƙamari.
A ranar 18 ga watan Yuni kaɗai, rahoton ya nuna an samu sabbin masu kamuwa da cutar 236, yayin da mutum 226 ke karɓar magani a cibiyoyin lafiya daban-daban.
Masana kiwon lafiya na ci gaba da kira ga al’umma da su kiyaye tsaftar muhalli da ta abinci tare da amfani da tsaftataccen ruwa domin dakile yaɗuwar cutar a jihar.
