Connect with us

Opinion

Yadda HE Garo Ya Wakilci Gwamna Fiye Da Wadansu Mataimakan Da Gwamnoninsu Cikin Kwanaki 47

Published

on

images (12)

Yadda HE Garo Ya Wakilci Gwamna Fiye Da Wadansu Mataimakan Da Gwamnoninsu Cikin Kwanaki 47

— Yabo ga Gwamna wajen karfafa yarda da amana da zartaccen dogaro

Advertisement

 

Daga Abba Anwar 

Advertisement

 

Kamar dai yadda kowa ya sani ne, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tantance kuma ta tabbatar da Maigirma Murtala Sule Garo, a ranar 27 ga watan Afrilu, 2026. Bayan da tsohon Mataimakin Gwamna Maigirma Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye aiki dan kashin kansa.

Advertisement

Bayan nan kuma sai a ka rantsar da Garo ranar 5 ga watan Mayu, 2026. Daga lokacin zuwa yau 20 ga watan Mayu, ya cika kwanaki 47 cif a kan karagar mulki kenan.

 

Advertisement

Daga lokacin da a ka rantsar da shi zuwa yanzu ya wakilci Gwamna Maigirma Abba Kabir Yusuf a wurare da yawan gaske. Ban sa wurare irin na gaisuwar mara lafiya da gaishe-gaishen mutuwa da daure-dauren aure ba. Saboda tun ma kafin lokacin ya zama Mataimakin Gwamna dama yin hakan dabi’arsa ce.

 

Advertisement

Kafin in nutsa cikin ire-iren wuraren da ya wakilci Gwamna din, zan fara da cewar, dama tun daga ranar rantsuwarsa, bayanin da ya yi a wajen ya nuna sakankancewar sa ga sabon tsarin nan na “Kano First Agenda.” Kan abubuwan da su ka shafi kyautata harkokin lafiya da ilimi da noma da samar da aikin yi ga al’umma.

 

Advertisement

Tun daga jawabin sa na karbar wannan mukami, ya nuna a fayyace cewar, shi fa mabiyi ne mai biyayya da karbar umarni ba wata tangarda. To tun daga nan fa ya aza harshashin kyakkyawar alaka tsakanin sa da Maigirma Gwamna.

 

Advertisement

Wani babban abin lura kuma shine daidai lokacin da wasu da yawa daga cikin Mataimakan Gwamnoni na wasu jihohin su ka wakilci Gwamnoninsu sau uku ko sau biyu ko sau daya ko ba ko daya ma, a cikin wadannan kwanaki 47, shi kuma a daidai lokacin ya wakilci Gwamna Yusuf sau wajen 10.

 

Advertisement

Hakan da nake fada, ba kuma wai ina tuhumar ragowar Mataimakan Gwamnonin ba ne. A’a sai dai kawai ina kwatanta yawan wakilcinsu ne da na Maigirma Garo a wadannan kwanaki 47. Ba dadi ba ragi. Illa iyaka.

 

Advertisement

Ranar 8 ga watan Yuni, ya wakilci Gwamna lokacin da Jakadun Kungiyar Gamayyar Turai, wato “European Union (EU) Ambassadors” su ka kai ziyarar ban girma gidan gwamnatin jihar Kano. Washegari kuma 8 ga watan Yuni din, ya kara wakiltar Gwamna wajen taron Gwamnonin Arewa Maso Yamma tare da wadannan Jakadu, kan abubuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiya da cigaban kasa.

 

Advertisement

Ranar 13 ga watan Yuni ya wakilci Gwamna a rufe wata gasar kwallon kafa da a ka yi a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata. Karkashin shirin “North-West Veterans All-Star Renewed Hope.”

 

Advertisement

A wani bikin yaye dalibai a makarantar sojojin ruwa dake karamar hukumar Dawakin Tofa, wato “Navy Logistics College,” wanda a ka yi ranar 18 ga watan Yuni, Maigirma Mataimakin Gwamna ya wakilci Gwamna a wajen. A matsayin babban bako. Jawabin da ya yi a wajen kuma ya kara tsima dakarun sojojin kan aikinsu da kishin kasa.

 

Advertisement

A wani kirari da na yi masa a halin da a ke ciki shine, “Garo Ka Iya Mataimakin Gwamna,” ya kara wakiltar Gwamna a ranar 27 ga watan Mayu, lokacin da ya kaddamar da wani shirin NNPC da ya shafi harkar iskar Gas na kamfanin Kanawa Gas Ltd.

 

Advertisement

Wani babban abin lura kuma shine, lokacin da wasu Mataimakan Gwamnonin shiyyoyi shida na kasar nan ke da tarihin wakiltar Gwamnonin su sau uku uku ko biyu ko dai-dai, wasu ma ba wannan maganar, a cikin kwanaki 47, amman shi Maigirma Garo ya wakilci Gwamna har sau kusan 10.

 

Advertisement

A daidai hakan ne kuma ya wakilci Gwamna a wani taron Gwamnonin Arewa Maso Yamma kan tsaro, wanda kungiyar Gwamnonin shiyyar su ka shirya. An yi taron ne ranar 29 ga watan Mayu, a jihar Kaduna.

 

Advertisement

A asibitin Hasiya Bayero kuma lokacin da a ka kaddamar da shirin samarwa asibitin gadon marasa lafiya guda Dari Biyar (500), bangaren yara da mata, ya wakilci Gwamna a wajen. An yi bikin ne ranar 3 ga watan Yuni.

 

Advertisement

Sannan kuma ya wakilci Gwamna wajen yin wani gagarumin taro da kungiyoyi masu zaman kansu kan harkar kasafin kudi da inganta aiki da shi. Wanda a ka yi ranar 7 ga watan Yuni din dai.

 

Advertisement

Ranar Dimukuradiyya kuma, wato 12 ga watan Yuni, ya kara wakiltar Gwamna a wajen bikin da a ka yi a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. Lokacin da har addu’o’i an yi wa kasa.

 

Advertisement

Maigirma Garo ya je wajen duba aikin titin Kwanar Dangora-Zaria da na Dala-Kofar Mata, a madadin Gwamna, wanda a ka yi ranar 15 ga watan Yuni. Yayin da ya karawa masu yin aikin kaimi wajen ganin sun hanzarta kammala aikin.

 

Advertisement

Sai kuma ranar 18 ga watan Yuni din dai ya je wani taro da masarauta a Gidan Rumfa kan shirye-shiryen bukukuwan Sallah cikin tsaro da kwanciyar hankali. A wajen taron ma ya wakilci Maigirma Gwamna ne.

 

Advertisement

Saboda kuma na kara jan hankalin masu karatu su san cewa akwai aminci da yarda tsakanin Gwamnan Kano da Mataimakin sa, sai na yi bincike kan yadda wasu Mataimakan Gwamnanonin shiyyoyi 6 na kasar ne suke kan abinda ya shafi wakiltar Gwamnoninmu. A cikin wadannan kwanaki 47.

 

Advertisement

Amman fa yin hakan ba ya nufin ina kallon su da wani abu ba. Kawai dai so nake na danganta yadda kyawun alaka da sakankancewa da juna dake tsakanin Gwamnan Kano da Mataimakin sa. Tun daga lokacin da a ka rantsar da shi abin ya fara daga kyakkyawan tushe.

 

Advertisement

Bari na fara da Arewa Maso Yamma tukuna. Dama na fara da maganar Maigirma Garo. Saboda haka bari na fara da Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, wato Maigirma Hadiza Sabuwa Balarabe.

 

Advertisement

Maigirma Balarabe ta wakilci Gwamna Uba Sani sau uku a wadannan kwanakin da nake magana. A ranar 18 ga watan Mayu, ta wakilci Gwamna a wani gagarumin taron da ya shafi cigaban jihohin Arewa Maso Yamma. Haka nan kuma a dai cikin watan na Mayu ne ta kara wakiltar Gwamnan a wajen kaddamar da tashin maniyyata aikin Hajji a sansanin Alhazai na Mando. Na ukun kuma shine da ta wakilce shi a filin wasa na Kafanchan wajen kaddamar da takarar Sanata Sunday Marshall Katung.

 

Advertisement

A sashen Arewa Maso Gabas kuma, misali a jihar Bauchi, Mataimakin Gwamna Maigirma Auwal Jatau, ya wakilci Gwamnan sa sau uku a wadannan kwanaki da nake magana a kai. Ranar 3 ga watan Yuni ta wakilci Gwamna a taron Hukumar Raya Arewa Maso Gabas, wato “North East Development Commission.” Da kuma babbar makarantar nan ta kauyen Dungal. Sannan ranar 1 ga watan Mayu ya wakilci Gwamna wajen kaddamar da shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa Maso Gabas.

 

Advertisement

A jihar Adamawa kuma Mataimakin Gwamna Farfesa Kaletapwa George Farauta ya wakilci Gwamna wajen shirin tallafawa jama’a na “PAWECA Fintiri Business Wallet Phase 4 Disbursement,” a garin Yola.

 

Advertisement

Ya kara wakiltar sa a wajen bikin nadin sarauta na mutanen Batta, a fadar Hama Bata, a garin Demsa. Sau kuma lokacin nada sababbin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati da kuma nada wani Kantoma, a Yola.

 

Advertisement

Sannan a Arewa Ta Tsakiya kuma na dauki jihohin Nassarawa da Benue. Mataimakin Gwamnan Nassarawa Dr Emmanuel Agbadu Akabe ya wakilci Gwamna lokacin kaddamar da wani shiri na bayar da tallafin kudi ga mata, wato “Rural Women Special Cash Grant.” Da a ka yi a dakin taro na Akwe Doma, a garin lafiya. Sannan kuma ya wakilci Gwamna zuwa babban ofishin jam’iyyar APC na kasa.

 

Advertisement

A jihar Benue kuma Mataimakin Gwamna Dr Samuel Ode, mni, ya je bikin harkokin noma, wato “Agricultural Mechanisation Outgrower Programme,” da a ka yi a babban birnin jihar, Makurdi. Sai kuma wata walima da a ka a kwalejin sojoji “Armed Forces Command & Staff College,” a Makurdi din dai. Ya kuma wakilci Gwamna wajen hira da yan jarida kan taron sasantawa na jam’iyyar APC a jihar. Bayan nan sai wakilci wajen bikin binne Mama Elizabeth Apochi, a garin Owukpa, cikin karamar hukumar Ogbadibo.

 

Advertisement

A shiyyar Kudu Maso Yamma Mataimakin Gwamnan Osun Maigirma Kola Adewusi ya wakilci Gwamnansa ranar 18 ga watan Yuni a wani taron DAWN, da a ka shirya ma shugabannin ma’aikatan gwamnatocin Kudu Maso Yamma. Sai kuma a lokacin da kungiyar Gwamnonin shiyyar ta shirya taron Mataimakan Gwamnonin shiyyar kan hadin kan yankin.

 

Advertisement

Ranar 5 ga watan Yuni Mataimakin Gwamnan dai ya wakilci Gwamnan a wani taron lafiya na “Osun Art Surge HIV Project” a garin Osogbo. Da wani taron ma na lafiya na “US CDC/PEPFAR-funded HIV/AIDS project.” Lokacin da kwamitin neman zaben Gwamna Adeleke ya kai ziyarar ban girma ga fadar Ooni na Ife a Ile-Ife, Mataimakan Gwamna ne ya wakilci Gwamna a wajen.

 

Advertisement

A jihar Lagos kuma Mataimakin Gwamna Maigirma Obafemi Hamzat sau daya ya wakilci Gwamna a cikin wadannan kwanakin da muke magana a kai. Shine lokacin da a ka yi bikin ranar ma’aikata, wato 1 ga watan Mayu, a filin wasa na Onikan. Amman bincike ya nuna cewar shi Hamzat ya na ta abubuwan da su ka shafi takarar sa ta gwamna ne a shekarar 2027 mai zuwa.

 

Advertisement

A shiyyar Kudu Maso Gabas kuma a jihar Enugu, Mataimakin Gwamna Maigirma Ifeanyi Ossai, ranar 10 ga watan Yuni ya wakilci Gwamnansa a wajen kaddamar da neman takarar Sanata mai wakiltar Enugu North, a zaben cike gurbi, da a ka yi a karamar hukumar Igbo-Etiti

 

Advertisement

Sannan a jihar Abia kuma Mataimakin Gwamna Maigirma Ikechukwu Emetu, a ranar 1 ga watan Mayu ya wakilci Gwamna a wajen taron duban gyaran tsarin mulki na kasa daga mahangar Kudu Maso Gabas.

 

Advertisement

Daga bangaren Kudu Maso Kudu kuma Mataimakin Gwamnan jihar Cross River Peter Odey a ranar 14 ga watan Mayu ya wakilci Gwamna a taron Majalisar Zartaswa ta Jiha, da a ka yi a ofishin Gwamna.

 

Advertisement

A jihar Rivers kuma Mataimakin Gwamna Maigirma Ngozi Odu ta wakilci Gwamna a ranar ma’aikata, wato 1 ga watan Mayu. Da a yi a Isaac Boro Park, na Port Harcourt.

 

Advertisement

Maganar dai gaba daya a nan ita ce, lokacin da wasu daga cikin Mataimaka Gwamnoni ba sa samun dama daga wajen Gwamnonin su na wakilcin su. Duk lokacin da su Gwamnonin ba sa gari. Sai kuma wata rana su tura Shugabannin Majalisun jihohin nasu su wakilce su. Yayin da watakila da gangan za ka ga sun tura Mataimakan nasu wani abu a wajen jihohin. Amman fa a jihar Kano abin ba haka yake ba. Ya sha banban da abinda a ke gani a wasu jihohi. Wannan abin a yabawa Maigirma Gwamna Yusuf ne.

 

Advertisement

Kuma duk wanda ya yi nazarin yadda Gwamna Yusuf yake tura Mataimakinsa Garo wakilci a wurare da dama haka a cikin wadannan kwanaki 47, hakan na nuni da cewa tabbas Juma’ar da za ta yi kyau daga Laraba a ke gane ta. Ba abinda ya rage mana a matsayin mabiya sai addu’ar Allah Ya ci gaba da hada kansu, wajen kawo ayyukan ci gaban wannan jiha ta mu mai albarka. A gaba dayan zango mulkinsu.

 

Advertisement

Anwar ya rubuto wannan daga Kano

Lahadi, 21 ga watan Mayu, 2026

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending