News
ICPC Ta Bankado Sabbin Hukumomin Bogi Biyu Yayin Bincike Kan PFIPC
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (ICPC) ta ce ta gano wasu ƙarin hukumomin gwamnati na bogi guda biyu yayin ci gaba da binciken da take yi kan abin da ake kira Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC)
Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan bayan gabatar wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, rahoton wucin-gadi na binciken da hukumar ta gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Aliyu ya ce binciken ya tabbatar da cewa Adeniyi Matthew Adeyemi, wanda ya riƙa bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na PFIPC, bai taɓa samun naɗi daga Gwamnatin Tarayya ba, yayin da ita kanta hukumar PFIPC ba ta da wata kafa ta doka.
Ya ƙara da cewa takardar naɗin da Adeyemi ya riƙa amfani da ita ta bogi ce, sannan ya mamaye ofisoshi da kayayyakin tsohuwar Presidential Economic Advisory Council (PEAC) ba tare da izini ba.
A cewar shugaban ICPC, binciken ya kuma gano wasu hukumomin bogi guda biyu da suka haɗa da FCT Investment Promotion Agency da Foreign Investment Promotion Agency, waɗanda aka ce an ƙirƙire su ta amfani da takardun doka na bogi.
Ya ce an yi amfani da waɗannan hukumomi wajen buɗe asusun bankuna domin gudanar da haramtattun ayyuka.
Aliyu ya bayyana cewa daga baya Adeyemi ya sauya sunan hukumar daga Foreign Investment Promotion Council zuwa Foreign Intervention Promotion Council, domin faɗaɗa ayyukanta har da batun tara kuɗaɗen shiga.
Rahoton ICPC ya nuna cewa babu wata kuɗaɗen gwamnati da aka ware ko aka fitar domin PFIPC ko PEAC, tare da tabbatar da cewa babu wata matsala da aka samu a tsarin Fadar Shugaban Ƙasa ko na Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Hukumar ta ba da shawarar gurfanar da Adeyemi a gaban kotu, tare da ɗaukar matakin ladabtarwa kan jami’an gwamnati da ake zargin sun taimaka wajen gudanar da ayyukan hukumar bogin.
Aliyu ya ce binciken bai kammala ba, yana mai cewa ana ci gaba da tattara ƙarin hujjoji domin gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a lamarin.
Ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu ya karɓi rahoton binciken, tare da sake jaddada aniyar gwamnatin tarayya na yaƙi da cin hanci da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a hukumomin gwamnati.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
