News
Akwai Yiwuwar Fuskantar Ɓullar Cutar Ebola Kowanne Lokaci Daga Yanzu — Gwamnatin Tarayya
Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta fitar da gargaɗin da ke nuna cewa ƙasar na cikin haɗarin yiwuwar fuskantar ɓullar cutar Ebola kowanne lokaci daga yanzu.
NCDC wadda ta ce tuntuni jami’anta na cikin shirin tunƙarar wannan cuta da ake ganin yaɗuwarta a Congo tun bayan sake ɓarkewarta a watan Mayun shekarar nan da kawo yanzu ta kashe mutane fiye da dubu 3 da 699, kodayake har kawo yanzu bata fantsama wata ƙasa a yankin yammacin nahiyar ta Afrika ba.
TINUBU DA SHETTIMA BA SA NAJERIYA — “Ba Ni Ne Mukaddashin Shugaban Ƙasa Ba” — Akpabio
Sanarwar da NCDC ta fitar a jiya Laraba mai ɗauke da sa hannun Jide Idris, ta ce bayan gano barazanar yiwuwar ɓullar cutar, jami’anta sun ƙara ƙaimi wajen ganin sun baiwa lafiyar jama’ar Najeriyar kariya daga cutar mai haɗari.
Sanarwar ta ce jami’an hukumar na ɗaukar dukkanin matakan da zasu iya wajen ganin ba a samu ɓarkewar Ebola a Najeriya ba, kodayake dole sai da haɗin gwiwar ɗaiɗaikun jama’a da kuma sauran hukumomin da haƙƙin kare jama’a ya rataya a wuyansu.
A cewar NCDC, wajibi ne gudanar da gwaje-gwajen lafiya kan dukkanin matafiyan da suka shigo Najeriyar daga ƙetare musamman daga ƙasashen da ake da fargabar yiwuwar cutar ta isa.
Haka zalika NCDC ta ce hatta a tsakankanin jama’ar gari ya zama wajibi su sanya idanu ga duk wanda suka samu da alamun cutar ta Ebola don gaggauta miƙa kai ga masana kiwon lafiya.
A cewar NCDC fitar da gargaɗi kan cutar ta Ebola ya biyo bayan mabanbantan tattaunawa da ƙwararru a fannin da kuma hukumar lafiya ta Najeriyar bayan nazartar halin da ake ciki a ƙasar yanzu haka.
Wasu daga cikin alamomin cutar ta Ebola a cewar ƙwararru akwai mashasshara kana ciwon kai mai tsanani sai kuma ciwon gaɓobi da kasala ko ciwon maƙogwaro kana rashin sha’awar abinci yayinda idan ta tsananta wato bayan kwanaki 4 zuwa 5 a jikin mutum kan kai ga haraswa ko gudawa a wasu lokutan har da zubar jini kan ƙuraje a jiki da kuma sauyawar kalar ido.
Zuwa yanzu mutane dubu 7 da 672 cutar ta Ebola ta harba a sassan jamhuriyyar Congo a wani yanayi da cutar ta ɓullla zuwa Larduna 7 na ƙasar kodayake a farkon makon nan an faro allurar rigakafin cutar mai suna Ervebo.
Tun bayan watan Yulin shekarar 2014 Najeriya bata sake samun ɓullar cutar ta Ebola ba, wadda a wancan lokaci ta kashe mutane 8 cikin mutane 20 da suka harbu ita bayan bayan wani fasinjan ƙetare ya sauka a jihar Lagos lamarin dsa ya sanya ganin cutar a jihar ta Lagos da kuma Fatakwal, kodayake a watan Oktoban shekarar WHO ta ayyana Najeriyar a sahun ƙasashen da basa ɗauke da masu cutar.
