News
Ya Kamata Kowane Dan Najeriya Ya Samu Horon Aikin Soja —Ministan tsaro
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ba da shawarar cewa a riƙa yi wa dukkan ’yan Najeriya horon aikin soja.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka wallafa ranar Litinin a shirin African Leadership Podcast na Ken Giami.
Akwai Yiwuwar Fuskantar Ɓullar Cutar Ebola Kowanne Lokaci Daga Yanzu — Gwamnatin Tarayya
Ya ce horon zai taimaka wa fararen hula fahimtar irin wahalhalun da sojoji ke fuskanta, ciki har da yunwa, gajiya, rashin barci da tafiya mai nisa a yanayi mai wahala.
Ya ce hakan zai sa jama’a su fahimci irin sadaukarwar da sojoji ke yi wajen kare ƙasa, ciki har da jefa rayukansu cikin haɗari.
Ministan ya kuma ce ya kamata ’yan Najeriya su yi la’akari da irin tsadar da ayyukan soji ke jawowa sojoji da iyalansu kafin su soki aikin da suke yi.
