Connect with us

News

An Daura Auren Khadija Ali Dan Abba Da Nazifi Yusuf Rabiu

Published

on

IMG 20260925 WA0358 1280x700

Daruruwan ’yan uwa da abokan arziki ne suka halarci ɗaurin auren Khadija Ali Dan Abba, ’yar Kwamishina na II na Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Sheikh Ali Dan Abba, da Nazifi Yusuf Rabiu.

An gudanar da ɗaurin auren ne a ranar Juma’a a Masallacin Hukumar Shari’a da ke Kano, inda aka tabbatar da auren bayan an biya sadakin da ya kai naira 250,000.

Ya Kamata Kowane Dan Najeriya Ya Samu Horon Aikin Soja —Ministan tsaro

Limamin da ya jagoranci ɗaurin auren ya shawarci sabbin ma’auratan da su gina rayuwar aurensu bisa soyayya, fahimtar juna da mutunta juna, kamar yadda koyarwar addinin Musulunci ta tanada.

Ya kuma bukaci ma’auratan da su kasance masu haƙuri da juriya wajen magance duk wani ƙalubale da ka iya tasowa a rayuwar aurensu, tare da fahimtar juna a kowane lokaci.

Da yake jawabi, mahaifin amaryar, Sheikh Ali Dan Abba, ya nuna godiyarsa ga ’yan uwa, abokai da sauran mahalarta bikin da suka halarci ɗaurin auren domin taya iyalinsa murnar wannan rana.

Advertisement

Sheikh Ali Dan Abba ya kuma gode wa dukkan waɗanda suka nuna ƙauna da goyon baya ga iyalinsa ta hanyar halartar bikin da kuma taya sabbin ma’auratan murna.

Daga bisani, mahalarta bikin sun yi addu’ar fatan alheri ga sabbin ma’auratan, tare da yi musu fatan samun zaman lafiya da ɗorewar aure.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending