Connect with us

News

Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 144 Domin Ayyukan Raya Kasa

Published

on

img 0773 (1)

Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 144.05 domin aiwatar da ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na jihar.

An amince da kuɗaɗen ne a taron majalisar karo na 41 da aka gudanar ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, a Malam Aminu Kano House da ke Asokoro, Abuja.

An Daura Auren Khadija Ali Dan Abba Da Nazifi Yusuf Rabiu

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dr Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kano.

Ya ce ayyukan sun haɗa da gina da gyaran hanyoyi, ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da makamashi, gidaje da sauran abubuwan more rayuwa.

A cewarsa, Ma’aikatar Ayyuka ce ta samu kaso mafi yawa, inda aka ware mata Naira biliyan 84.975 domin ayyukan hanyoyi da gine-ginen gwamnati.

Advertisement

Daga cikin hanyoyin da aka amince da aiwatar da ayyukansu akwai Rawul–Gani–Sitti–Masu–Gomo Road a Sumaila, Zaria Road–Gurjiya–Yankatsari–Rijiyar Gwangwan da Dawakin Kudu–Lahadin Makole Road.

Sauran ayyukan sun haɗa da wasu hanyoyi a Nassarawa GRA, Tarauni, Kumbotso da Janbulo.

Majalisar ta kuma ware Naira biliyan 14.276 ga fannin ilimi, yayin da aka ware Naira biliyan 2.608 ga fannin kiwon lafiya domin gyaran cibiyoyin lafiya da inganta asibitoci.

Haka kuma, Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane ta samu sama da Naira biliyan 11 domin aiwatar da wasu ayyuka, ciki har da samar da kayayyakin kula da zirga-zirga da inganta abubuwan more rayuwa.

A wani ɓangare na shawarar, majalisar ta amince da kasafin kuɗin kari na shekarar 2026 na Naira tiriliyan 1.201, inda ta umurci a miƙa ƙudirin ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin duba shi da amincewa.

Majalisar ta kuma amince da gudanar da Kano Art and Cultural Festival (KANFEST) 2026, tare da amincewa da shirin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin bunƙasa Kano Energy and SME Industrial Park da ke Tamburawa.

Advertisement

Bugu da ƙari, an umurci Ma’aikatar Ayyuka da ta duba hanyar Eastern Bypass zuwa Tsamiya Babba, Larabawar Abasawa da Nera Roundabout, domin tantance yiwuwar yaranta.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending