Connect with us

News

Africa Academy Hausa Ta Yaye Dalibai Sama Da 3,500

Published

on

IMG 8397

Africa Academy Hausa ta yaye ɗalibai sama da 3,500 daga Najeriya da sauran ƙasashe, a bikin yaye dalibai karo na biyu da aka gudanar a Kano.

‎An gudanar da bikin ne ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026, a Convocation Arena da ke  harabar Jami’ar Bayero, Kano (BUK New Site).

An Daura Auren Khadija Ali Dan Abba Da Nazifi Yusuf Rabiu

‎Da yake jawabi a wajen taron, Manajan Daraktan Africa Media Network, Dr Habib Tajjani Tahir, ya bayyana cewa makarantar na gudanar da karatu ne ta yanar gizo, abin da ya bai wa mutane daga wurare daban-daban damar samun ilimi ba tare da sai sun halarci aji kai tsaye ba.

‎Ya ce tsarin karatun ya bai wa ɗalibai damar yin karatu daga duk inda suke, tare da haɗa karatu da sauran ayyukan rayuwarsu.

‎Dr Tahir ya ce ɗaya daga cikin manufofin shirin shi ne bai wa ɗalibai ilimin da zai taimaka musu wajen sanin yadda za su bautawa Allah Madaukakin Sarki da kuma amfani da ilimin wajen inganta rayuwarsu.

Advertisement

‎A yayin bikin, ɗaliban da suka kammala karatun sun bayyana farin cikinsu, inda suka ce sun ji daɗin ganin sun samu nasarar kammala karatun da suka shafe lokaci suna yi ta yanar gizo.

‎Wasu daga cikin ɗaliban sun bayyana cewa tsarin karatun ya sauƙaƙa musu samun ilimi, musamman ganin cewa suna iya yin karatun daga gidajensu ko wuraren da suke, ba tare da katse ayyukansu na yau da kullum ba.

‎Sun kuma bayyana cewa bikin yaye daliban ya kasance wata muhimmiyar rana a gare su, domin ya ba su damar haɗuwa da sauran ɗalibai da malamansu tare da nuna farin cikinsu bayan kammala karatun.

‎Wasu daga cikinsu sun ce za su ci gaba da neman ƙarin ilimi tare da amfani da abin da suka koya wajen taimaka wa kansu da al’umma.

‎Haka kuma, an sanar da wasu kyaututtuka ga ɗaliban da suka yi fice a karatun, inda aka bayyana cewa ɗaliban da suka zo daga matsayi na Daya zuwa na Biyar su samu kyautar samu kyautar kujirar Umara da biyar zuwa na 13 za su samu kyautar dala 100.

‎Bikin ya kuma kasance wata dama ga ɗaliban da suka kammala karatun na Africa Academy Hausa wajen gudanar da bukukuwan nasarar da suka samu tare da iyalansu da abokansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending