News
Akalla Mutane 259 Ne Suka Mutu Sakamakon Zazzabin Lassa A Najeriya
Akalla mutane 259 ne suka mutu sakamakon zazzabin Lassa a Najeriya tun daga farkon shekarar 2026 zuwa yanzu, yayin da mutane 1,086 suka kamu da cutar.
Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta bayyana hakan a sabon rahotonta kan halin da cutar ke ciki a kasar.
TINUBU DA SHETTIMA BA SA NAJERIYA — “Ba Ni Ne Mukaddashin Shugaban Ƙasa Ba” — Akpabio
A cewar hukumar, an samu masu dauke da cutar a kananan hukumomi 118 da ke cikin jihohi 24 na Najeriya.
Rahoton, wanda ya shafi mako na 36 na yaduwar cutar, daga ranar 31 ga Agusta zuwa 6 ga Satumba, ya nuna cewa yawan mace-macen da cutar ta haddasa ya kai kashi 23.9 cikin 100.
NCDC ta ce wannan adadi ya fi na makamancin lokacin shekarar 2025, inda yawan mace-macen ya kasance kashi 18.6 cikin 100.
Hukumar ta ce an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar daga mutum 18 a mako na 35 zuwa mutum 12 a mako na 36.
Sai dai jimillar masu kamuwa da cutar ta karu daga 1,074 zuwa 1,086, yayin da aka samu karin mutum guda cikin wadanda suka mutu.
NCDC ta ce jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Benuwai da Edo ne suka samar da kashi 87 cikin 100 na masu kamuwa da cutar a mako na 36.
A wannan makon kuma, an samu sabbin masu kamuwa da cutar 12 a jihohin Ondo, Edo da Kogi, yayin da babu wani jami’in lafiya da aka samu yana dauke da cutar.
A mako na 35 kuwa, mutane 18 ne suka kamu da zazzabin Lassa a jihohin Ondo, Edo da Bauchi.
Abubuwan da ke kara yaduwar cutar
NCDC ta ce rashin tsaftar muhalli, karancin wayar da kan jama’a da kuma jinkirin zuwa asibiti na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen yaduwar zazzabin Lassa.
Hukumar ta bukaci jihohin da cutar ta fi kamari da su kara kokarin wayar da kan jama’a kan hanyoyin kare kai daga cutar da kuma muhimmancin tsaftace muhalli.
Haka kuma, ta bukaci ma’aikatan lafiya da su rika gano alamun cutar cikin gaggawa tare da daukar matakan kariya yayin kula da masu dauke da ita.
