News
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙi da aikata laifuka, inda jami’anta suka dakile wani yunƙurin fashi da makami tare da kama wasu da ake zargi da sace wani jariri.
Mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 3:00 na safiyar Alhamis, jami’an Sashen Yaƙi da Manyan Laifuka (VCRU) sun yi artabu da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a unguwar Danmasara da ke Dutse.
ICPC Ta Bankado Sabbin Hukumomin Bogi Biyu Yayin Bincike Kan PFIPC
Bayan bin motarsu da suka yi, waɗanda ake zargin sun bude wa jami’an wuta kafin su tsere cikin daji. Daya daga cikinsu ya samu raunuka kuma ya rasu a asibiti, yayin da aka kwato adduna biyu, sanduna uku, igiyoyi da wayar salula.
A wani samame na daban, rundunar ta ceto wani jariri mai shekara ɗaya da rabi da aka sace daga Asibitin Babura.
An kama Khadija Aliyu mai shekaru 20 da jaririn a hannunta, sannan bincike ya kai ga cafke Sadik Sale Yahaya, ma’aikacin jinya a Asibitin Babura, bisa zargin haɗa baki wajen satar jaririn.
Wacce ake zargin ta amsa cewa ta yi shirin sayar da jaririn kan kuɗi Naira miliyan biyu.
Rundunar ta ce an tsare jaririn cikin aminci kuma za a mayar da shi ga iyayensa bayan kammala bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya yaba da ƙwazon jami’an tare da ƙarfafa gwiwar al’umma su ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai domin yaƙi da aikata laifuka.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
