News
Gwamna Abba Ya Samu Kyautar WINSEC, Waiya Ya Lashe Lambar Yabo Kan Dabarun Sadarwa
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samu Kyautar Girmamawa ta Women in Security Summit (WINSEC) 2026 bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari.
An ba da kyautar ne a taron WINSEC na shekarar 2026 da Ƙungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NAWOJ) ta shirya a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja.
Shugaba Tinubu Ya Umurci EFCC Ta Bude Asusun Bankin Gwamnatin Jihar Osun Da Ta Kulle
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya wakilci gwamnan tare da karɓar kyautar a madadinsa.
Da yake jawabi bayan karɓar lambar yabon, Waiya ya ce wannan karramawa ta nuna irin yadda ake yaba wa salon jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman a fannonin kyautata rayuwar al’umma, tabbatar da zaman lafiya da inganta ayyukan gwamnati.
Ya gode wa masu shirya taron a madadin gwamnatin Kano da al’ummar jihar, yana mai cewa wannan karramawa za ta ƙara wa gwamnati ƙwarin gwiwar ci gaba da gudanar da mulki bisa gaskiya, riƙon amana da hidima ga jama’a.
Waiya ya kuma bayyana cewa kyautar ta samo asali ne daga hangen nesa da jajircewar gwamnan wajen aiwatar da manufofin da ke kawo ci gaba da walwalar al’umma.
A wani ci gaba kuma, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya samu Lambar Yabo ta Ƙwarewa Kan Dabarun Sadarwa (Strategic Communication Award) daga NAWOJ, bisa rawar da yake takawa wajen isar da manufofi da ayyukan gwamnatin Kano ga al’umma cikin ƙwarewa.
Da yake karɓar lambar yabon, Waiya ya gode wa NAWOJ bisa karramawar da ta yi masa da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa hakan zai ƙara masa himma wajen ci gaba da inganta harkokin sadarwa da gudanar da ayyukan gwamnati.
Ya kuma gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa wannan tagomashi, tare da jaddada cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta domin tabbatar da ci gaba da walwalar al’ummar jihar.
