Connect with us

Uncategorized

An Kama Wani Mutum Bisa Zargin Jagorantar Masu Satar Wayoyi A Kano

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar yaƙi da fadan daba da kwacen waya ta Jihar Kano ta kama wani matashi da aka fi sani da Ali Baban Jakai, bisa zargin jagorantar gungun matasa masu satar wayoyi da kuɗaɗen jama’a a kasuwannin Bata da Ƴan Kura.

Kwamandan rundunar, CMD Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan rediyon Dala FM da ke Kano a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026.

Gwamnatin Lagos Ta Rufe Wata Coci Saboda Damun Mutane Da Hayaniya

Ya bayyana cewa cafke Ali Baban Jakai ya biyo bayan kama wasu matasa 10 da ake zargi da aikata satar wayoyi da kuɗaɗe a kasuwannin, inda suka ambaci sunansa a matsayin wanda ke jagorantarsu.

A cewarsa, jami’an rundunar ta Operation Phone Snatching ne suka cafke wanda ake zargin a yankin Sabon Gari da ke Kano.

Da yake mayar da martani kan zargin, Ali Baban Jakai ya amsa cewa a baya ya taɓa shiga harkar satar wayoyi da kuɗaɗen jama’a, inda ya shafe sama da shekaru shida yana wannan sana’a, amma ya ce ya daina.

Advertisement

Sai dai ya musanta zargin cewa shi ne jagoran matasan da aka kama, duk da cewa ya tabbatar da sanin wasu daga cikinsu.

Kwamandan rundunar ya ce za su miƙa wanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakanda suka dace.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending